Ana Wata ga Wata: Ministan Shari'a Ya Nemi a Soke Rajistar ADC, Wasu Jam'iyyu 4

Ana Wata ga Wata: Ministan Shari'a Ya Nemi a Soke Rajistar ADC, Wasu Jam'iyyu 4

  • Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari'a na kasa, Lateef Fagbemi ya yi kira a soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa
  • Daga cikin jam'iyyun da ake so a soke akwai babbar jam'iyyar adawa ta ADC da ta sha alwashin kifar da Bola Tinubu a zaben 2027
  • Lateef Fagbemi ya bayyana cewa jam'iyyun da ake nema hukumar zabe ta kasa (INEC) ta soke su ba su cika ka'idar rajista ba a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban lauyan gwamnatin Najeriya ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tilasta wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) soke rajistar jam’iyyu biyar.

Lateef Fagbemi SAN ya yi korafi yana mai cewa ci gaba da wanzuwarsu ya saba wa kundin tsarin mulki kuma yana raunana sahihancin tsarin zaben Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Shettima ya yi gargadi kan rusa APC bayan zaben fitar da gwani

Ministan shari'a, Lateef Fagbemi
Babban lauyan Gwamnatin Najeriya, Lateef Fagbemi. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Bukatar soke rajistar ADC da wasu jam'iyyu

Tribune ta rahoto cewa masu kara sun ce idan ba a dauki mataki ba, INEC za ta ci gaba da karya alhakin da kundin tsarin mulki ya daura mata ta hanyar barin jam’iyyun da ba su cika sharudan doka ba su ci gaba da kasancewa.

Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026, wadda aka shigar a sashen Abuja na Babbar Kotun Tarayya, ta lissafa Kungiyar Tsofaffin ‘Yan Majalisa ta Kasa a matsayin mai kara.

Wadanda ake kara sun hada da INEC a matsayin wanda ake kara na farko da Babban Lauyan Tarayya a matsayin na biyu, tare da jam’iyyu biyar: ADC, AA, APP, Accord da ZLP.

Muhimmin batu a neman soke jam'iyyar ADC

Muhimmin batu a shari’ar shi ne ko INEC tana da damar cire jam’iyyun da ba su cika sharadin nasarar lashe zabe da aka gindaya a Sashe na 225A na kundin tsarin mulkin 1999 ba.

Kara karanta wannan

Ana jiran hukuncin kotu: David Mark ya fadi abin da zai faru da ADC a zaben 2027

Masu karar sun ce jam’iyyun da abin ya shafa sun kasa cika ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada domin ci gaba da wanzuwar rajistarsu.

Shugabannin ADC yayin zanga-zanga a Abuja
Yadda manyan 'yan ADC suka yi zanga-zanga a Abuja. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Daga cikin wadannan ka’idoji akwai samun akalla kashi 25 cikin 100 na kuri’u a jiha a zaben shugaban kasa, ko kuma samun a kalla kujera daya ta zabe a matakin kasa, jiha ko karamar hukuma.

Sun kara da cewa jam’iyyun sun yi baya sosai a zaben gama gari na 2023 da kuma zabukan cike gurbi da suka biyo baya, inda suka kasa samun kujeru a muhimman matakan gwamnati.

Ministan shari'a ya goyi bayan karar

A cikin sanarwar da aka gabatar, babban lauyan tarayya, wanda shi ma yana cikin wadanda ake kara, ya amince da hujjojin masu kara gwargwadon nauyin da kundin tsarin mulki ya daura masa.

Lateef Fagbemi ya ce a matsayinsa na babban jami’in doka na kasa, wajibi ne a kansa ya tabbatar da bin kundin tsarin mulki, ciki har da tabbatar da bin dokar zabe da sauran dokokin da ke jagorantar zabuka a Najeriya.

Yayin da ADC ke cigaba da shiga rudani, Punch ta wallafa cewa a ranar 5 ga watan Mayun 2026 kotun za ta fara sauraron shari'ar.

Kara karanta wannan

Kotu ta rikita lissafin 'yan adawa, ta hana INEC amincewa da tarukan jam'iyyar ADC

'Za mu kifar da Bola Tinubu,' ADC

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar ADC a Kudu maso Yamma ta sha alwashin kifar da Shugaban kasa Bola Tinubu a 2027.

Shugabannin jam'iyyar a yankin sun bayyana cewa shugaban kasar bai kawo wani cigaba ba tun da ya fara mulkin Najeriya a 2023.

Saboda haka suka ce za su yi tsayuwar daka wajen ganin bai samu kuri'u ba a jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya da Tinubu ya fito.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng