2027: Abin da Mabiyan Peter Obi Suka Yi Ya Fara Jawo Wa Kwankwaso Matsala a Arewa

2027: Abin da Mabiyan Peter Obi Suka Yi Ya Fara Jawo Wa Kwankwaso Matsala a Arewa

  • Matasan Arewa sun fara kalubalantar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso kan kawancen da ya kulla da Peter Obi
  • Wata kungiyar matasa ta soki shirun Kwankwaso kan zargin cin mutuncin da magoya bayan Obi suka yi wa Sardaunan Sokoto da Dan Fodio
  • Ta ce alamu sun nuna cewa kawancen Obi da Kwankwaso ya fi karkata ga biyan bukatun siyasa da neman mulki fiye da kare muradun Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Kungiyar matasan Arewa ta Northern Youths Assembly ta yi watsi da kawancen tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da Peter Obi gabanin zaben 2027.

Peter Obi, tsohon dan takarar LP ya samu tikitin takarar shugaban kasa a NDC, kuma ya ayyana madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin mataimakin sa.

Kara karanta wannan

"Asiri zai tonu," Ana zargin ba tsakani da Allah Kwankwaso ya hada kai da Peter Obi ba

Keankwaso.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Rabiu Kwankwaso ya fara fuskantar matsala

Leadership ta ruwaito cewa kungiyar matasan ta bayyana wannan kawancen a matsayin cin amanar muradu da kimar siyasar Arewa.

Ta kuma kara da cewa hakan ya nuna shakku kan manufofin darikar Kwankwasiyya da Kwankwaso ke yawan bayyana wa, tare da ikirarin yana tafiya ne a kansu.

A wata sanarwa da sakataren kungiyar, Hafiz Garba, ya sanya wa hannu ranar Juma'a, ta zargi Kwankwaso da yin watsi da manufofin ci gaban Arewa, mutuncinta da kuma martabar al'adunta, wadanda suka kasance ginshikin tafiyar Kwankwasiyya.

Matasa sun fara zargin Kwankwaso

Kungiyar ta ce tafiyar Kwankwasiyya ta samu gagarumar karbuwa a fadin Arewa ne sakamakon shirye-shiryen ilimi, tallafawa al'umma da kuma fafutukar ci gaban yankin.

Ta kara da cewa alamar 'yan Kwankwasiyya watau jar hula ta samo asali ne daga kare muradun Arewa da kuma martabar tarihinta, kamar yadda Vanguard ta kawo.

A cewar kungiyar, wasu daga cikin masu goyon bayan tafiyar Obidient sun yi kalamai da ake kallon raini ne ga manyan jagororin Arewa da suka hada da Sir Ahmadu Bello, Abubakar Tafawa Balewa da Shehu Usmanu Dan Fodio.

Kara karanta wannan

Kwankwaso na shirin jagorantar zanga zanga kan rashin tsaro? An ji gaskiyar magana

An bukaci Kwankwaso ya yi bayani

Kungiyar ta tambayi dalilin da ya sa Kwankwaso bai fito fili ya kalubalanci irin wadannan ra'ayoyi ba kafin shiga kawancen siyasa da Peter Obi.

Sanarwar ta ce:

"Arewa na bukatar cikakken bayani daga Kwankwaso. Jagoran da ya gina tarihinsa na siyasa a kan alfaharin Arewa ba zai iya yin shiru ba yayin da ake cin mutuncin fitattun jaruman yankin."
Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

A cewarta, alamu sun nuna cewa kawancen Obi da Kwankwaso ya fi karkata ga biyan bukatun siyasa da neman mulki fiye da kare muradun al'ummar Arewa.

Ta gargadi cewa matakin na iya jawo rashin jin dadi a tsakanin masu goyon bayan da suka rungumi ainihin manufar Kwankwasiyya tun daga farko.

Kungiyar ta bayyana kawancen a matsayin kuskuren siyasa da zai iya raunana karfin Kwankwaso a wajen magoya bayansa na gargajiya a Arewacin Najeriya.

'Yan Obidient sun taba Sardauna da Dan Fodio?

Legit Hausa ba ta ci karo da inda magoya bayan Peter Obi suka taba iyayen da suka kafa Arewa ko Mujaddadin Musulunci, Usman Danfodio ba.

Kara karanta wannan

"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027

Sai dai wasu 'Yan Kwankwasiyya sun fito suna fifita madugunsu a kan Ahmadu Bello da Tafawa Balewa.

A dandalin Facebook, masoyan Kwankwaso musamman daga Kano sun zargi shugabannin farko da aka yi da kabilanci a kokarin tallata gwaninsu a zaben 2027.

Ayodele ya gargadi Obi kan Kwankwaso

Kun ji cewa babban malamin coci a Najeriya, Fasto Elijah Ayodele ya ja hankalin Peter Obi kan alakarsa da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Ayodele ya bayyana cewa kwadayin Peter Obi ya sa ya kasa lura da wasu abubuwan da ke faruwa a kusa da shi da za su iya kawo masa cikas a zaben 2027.

Ayodele ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya hada kai da tsohon gwamnan jihar Anambra ne domin cimma burinsa na kashin kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262