Obi Ya Fadi Darajar da Zai ba Kwankwaso a Matsayin Mataimakinsa bayan Nasararsu

Obi Ya Fadi Darajar da Zai ba Kwankwaso a Matsayin Mataimakinsa bayan Nasararsu

  • Dan takarar shgaban kasa a NDC, Peter Obi ya bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso ba zai zama dan kallo ba
  • Tsohon gwamnan ya ce shi da Kwankwaso za su yi aiki tare a matsayin abokan hulɗa masu cikakken iko wajen yanke muhimman shawarwari
  • Obi ya ce Kwankwaso yana da irin manufofinsa kan ilimi, tsaro da daidaito, yana mai alƙawarin kafa gwamnati mai haɗa kan kowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya yi karin haske kan yadda za su yi mulki da Rabiu Kwankwaso idan sun yi nasara.

Obi ya bayyana cewa zai kafa gwamnati mai haɗa kan kowa tare da Rabiu Musa Kwankwaso idan ya samu nasara a zaɓen 2027.

Peter Obi ya yi wa Kwankwaso alkawari
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) ya sanar da Kwankwaso a matsayin abokin takararsa a babban taron NDC da aka gudanar a Abuja, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Martanin Kwankwaso bayan samu tikitin takarar mataimakin Peter Obi a NDC

Yadda aka Obi, Kwankwaso suka fafata a 2023

Obi da Kwankwaso sun fafata a zaɓen shugaban ƙasa na baya, inda suka zo na uku da na huɗu bayan Atiku Abubakar da Shugaba Bola Tinubu.

Kwankwaso ya tsaya takara ne ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, inda ya lashe Kano kaɗai, jihar da har yanzu yake da ƙarfi da tasiri a siyasance.

Alkawarin da Obi ya yi ga Kwankwaso

Yayin da yake bayyana Kwankwaso a matsayin abokin takararsa, Obi ya ce ba zai jagoranci gwamnati wadda mataimakin shugaban ƙasa zai zama kamar dan kallo ba.

Ya ce gwamnatin da suke son kafawa za ta bai wa mataimakin shugaban ƙasa cikakkiyar damar zama abokin hulɗa wajen gudanar da mulki da yanke shawarwari.

Obi ya ƙara da cewa za a rika tattaunawa da kowa kafin yanke manyan matakai, yana mai cewa hakan ne tsarin mulki mai kyau yake buƙata, cewar Vanguard.

Daga nan ya amince da tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC tare da gayyatar Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya kasance abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya san matsayinsa da Peter Obi ya ayyana abokin takararsa na zaben 2027

Ya bayyana cewa Kwankwaso yana da irin manufofinsa, musamman wajen gina al'umma mai adalci inda ɗan talaka zai iya samun damar cimma nasara.

Peter Obi ya fadi yadda zai yi mulki da Kwankwaso
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Kwankwaso a taron jam'iyyar NDC a Abuja. Hoto: @SaifullahiHon.
Source: Twitter

Yadda Obi da Kwankwaso suka hada kai

Obi ya ce Kwankwaso ya yi imani da muhimmancin ilimi da tsaro, kuma za su yi aiki tare domin tabbatar da waɗannan manufofi sun zama gaskiya.

A ranar 3 ga Mayu, Obi da Kwankwaso sun koma jam'iyyar NDC bayan sun fice daga ADC, suna masu danganta matakin da rashin tabbas kan makomar jam'iyyar.

Tsohon gwamnan Anambra ya kuma sha alwashin yin wa'adi guda ɗaya na shekaru huɗu kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, tare da rage tsadar tafiyar da gwamnati.

Kwankwaso ya ji dadin zama mataimakin Obi

Mun ba ku labarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani bayan NDC ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.

Kwankwaso ya bayyana farin cikinsa da wannan dama, yana mai cewa amincewar da jam'iyyar da Peter Obi suka nuna masa babban abin alfahari ne.

Tsohon gwamnan Kano ya yabawa Sanata Seriake Dickson da shugabannin NDC, yana cewa matakin ya nuna ƙudirin haɗin kai da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.