‘Bai da Maraba da Buhari’: An Caccaki Tsarin Siyasar Peter Obi a Najeriya
- Wani mai fashin baki kan harkokin siyasa ya bayyana cewa matsalolin Najeriya sun fi karfin mutum guda ɗaya duba da matsalar kasar
- Masanin harkokin siyasar nan, Sola Kuti ya bayyana cewa tsarin siyasa ne babban kalubalen da ke hana ci gaba a Najeriya
- Ya ce ko shugaba mai kyakkyawar niyya zai fuskanci cikas daga masu ruwa da tsaki da tsarin da ke hana sauye-sauye masu ma'ana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fitaccen mai sharhi kan al’amuran jama’a da siyasa, Sola Kuti, ya yi magana kan matsalolin Najeriya da kuma hanyar shawo kansu.
Sola Kuti ya bayyana cewa matsalolin Najeriya ba wai suna da alaka da wanda ke mulki kadai ba ne, illa tsarin siyasar kasar.

Source: Twitter
An kwatanta tsarin siyasar Obi da ta Buhari
Yayin wata tattaunawa kan siyasa da TheCable ta bibiya, Kuti ya kwatanta dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ya gargadi 'yan Najeriya cewa suna iya sake fadawa cikin kuskuren da suka yi a baya na dora manyan buruka da tsammani kan mutum guda.
Kuti ya tuna cewa Buhari ya hau mulki ne tare da gagarumar goyon bayan jama'a, inda mutane da dama suka yi imanin zai kawo karshen cin hanci.
Sai dai ya ce gwamnatin Buhari ba ta kai ga cika irin manyan tsammanin da aka yi mata ba, duk da burin da jama'a suka ci.

Source: Twitter
Matsalar da Peter Obi ka iya fuskanta
A cewarsa, Peter Obi ma na iya fuskantar irin wannan yanayi, ba lallai saboda gazawar kansa ba, amma saboda matsalolin tsarin mulki.
Kuti ya yi bayanin cewa ko shugaba mai nagarta da kyakkyawar niyya zai samu kansa cikin matsin lamba daga masu anfani da tsarin da ke adawa da gyara.
Ya yi amfani da Buhari a matsayin misali, yana mai cewa duk da yadda mutane suka dauke shi mai gaskiya, bai kawo manyan sauye-sauye ba.
A ra'ayinsa, wannan ya nuna cewa matsalar tana cikin tsarin da ake tafiyar da kasa, ba wai mutum daya ne matsalar ba, cewar Leadership.
Babban sakon da Kuti ya isar shi ne cewa rikicin shugabanci da Najeriya ke fama da shi yana da alaka da tsarin siyasa gaba daya.
Ya ce muddin ba a sake fasalin tsarin ba, sauya shugabanni daga mutum zuwa wani ba zai haifar da sauyin da talakawa ke fata ba.
Kuti ya jaddada cewa gyaran tsarin mulki da siyasa shi ne mafita mafi dorewa domin samun ci gaba da sauyi mai amfani ga kasar.
Buhari ya shawarci Peter Obi kafin rasuwarsa
A wani labarin, an ji cewa an ruwaito cewa Peter Obi ya kai ziyara Daura domin ta’aziyyar Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana shi a matsayin shugaban da ya damu da talakawa.
'Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar LP a 2023, ya tuno haduwarsa da Buhari, wanda ya ce ba bar masa wasiyyar kula da 'yan kasar.
Obi ya ce har yanzu yana rike da wannan wasiyya ta Buhari, kuma yana ganin tsohon shugaban kasar ya yi kokari a lokacin mulkinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

