'Dan APC Ya Rasa Mukaminsa saboda Kiran Tinubu Ya Yi Murabus daga Kujerarsa

'Dan APC Ya Rasa Mukaminsa saboda Kiran Tinubu Ya Yi Murabus daga Kujerarsa

  • Gwamnatin Akwa Ibom ta sallami wani a ofishin Mmai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa bayan ya yi rubutu kan Bola Tinubu
  • Mutumin ya yi rubutu a kafofin sadarwa inda ya ce ya kamata Tinubu ya yi murabus saboda matsalolin ƙasa
  • Ya ce ya samu labarin sallamarsa ne ta kafafen sada zumunta bayan wasu mutane sun kira shi suka sanar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - An sallami wani hadimi a gwamnatin Akwa Ibom wanda ke ofishin mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa.

Gwamnatin Akwa Ibom ta dauki matakin ne bayan ya wallafa rubutu a kafofin sadarwa game gwamnatin Bola Tinubu.

An kori dan APC daga mukaminsa kan sukar Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Umo Eno a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Abin da ya jawo korar dan APC

Rahoton Premium Times ta ce Osborne Okon ya yi rubutu a Facebook cewa ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus.

Kara karanta wannan

INEC ta fara bincike, ta bankado bayanai kan hotunan da hadimin Ministan Abuja ya wallafa

Osborne Okon, ya rasa aikinsa ne bayan wata takarda mai dauke da sa hannun Godwin Ntuk Udeh, Mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa, ta sanar da dakatar da aikinsa nan take.

A cikin takardar sallamar, an bayyana cewa matakin ya biyo bayan wasu ayyuka da aka ce suna nuna rashin biyayya, tare da bukatar tabbatar da tsabtar ofishin.

Lamarin ya biyo bayan wani rubutu da Okon ya yi inda ya ce a kasa mai tsari, Tinubu da ya yi murabus cikin mutunci saboda halin da Najeriya ke ciki.

Ko da yake Okon dan jam'iyyar APC ne kamar shugaban kasa, kalamansa sun jawo ce-ce-ku-ce musamman ganin cewa Gwamna Umo Eno ya koma APC tare da nuna goyon baya ga Tinubu.

Gwamna ya fusata da wani dan APC ya caccaki Tinubu a kafar sadarwa
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom. Hoto: Pastor Umo Eno.
Source: Twitter

Abin da Okon ya ce kan sallamarsa

Da yake mayar da martani, Okon ya ce bai san da sallamarsa ba sai bayan wasu manyan mutane sun kira shi suna tambayarsa dalilin da ya sa aka dakatar da shi.

Ya bayyana cewa bayan ya duba Facebook ne ya ga takardar sallamar tana yawo a shafukan sada zumunta, lamarin da ya ba shi mamaki sosai.

Kara karanta wannan

Ana zargin gwamna Oyo da shirya sace dalibai don bata sunan Tinubu

Okon ya ce abin da ya fi ba shi mamaki shi ne zargin rashin biyayya, domin a cewarsa yana ofis tare da shugabansa har ranar da za a sallame shi.

Tsohon hadimin ya bayyana cewa dangantakarsa da Godwin Udeh ta fara tun kafin zaben gwamna Eno na shekarar 2023, kuma ba ta samo asali daga wata takardar aiki ba.

Ya ce ya ci gaba da aikin ne saboda yana sa ran samun damar ci gaba a gaba, ba wai saboda albashin N65,000 da ake biyansa kowane wata ba, cewar Daily Post.

A cewarsa, N65,000 ma ba wani albashi ba ne mai ma'ana a wannan lokaci na matsin tattalin arziki, yana mai cewa da kudi ne burinsa da tuni ya bar aikin.

Hadimin gwamnan Akwa Ibom ya ajiye mukaminsa

A baya, kun ji cewa hadimin Gwamna Umo Eno, Ndianaabasi Udom, ya yi murabus daga mukaminsu na shugabancin hukumar titunan karkara ta jihar Akwa Ibom.

Udom, wanda ke cikin kwamitin rikon PDP na jihar, bai bayyana dalilin murabus dinsa ba, sai dai ana alakanta haka da rikicin siyasa.

Siyasar jihar ta fara rincabe wa tun bayan da Gwamna Umo Eno ya fice daga PDP, tare da jan tawagarsa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.