INEC Ta Gano Yadda aka Haɗa Baki da Jami'inta wajen ba Hadimin Wike Bayanan Katin Zabe

INEC Ta Gano Yadda aka Haɗa Baki da Jami'inta wajen ba Hadimin Wike Bayanan Katin Zabe

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana yadda aka fitar da bayanan rajistar zaɓen jarumi Emeka Ike ba bisa ka’ida ba
  • Lere Olayinka, hadimin Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fallasa bayanan katin zaben Emeka Ike, lamarin da ya haifar da cece-kuce a Najeriya
  • Hukumar INEC ta fito da bayanai daga baya, inda ta bayyana cewa wannan al'amari ba kutse aka yi wa na'urarta ba, mika bayanan aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja — Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi bayani kan yadda mai magana da yawun Ministan Abuja, Lere Olayinka, ya samu bayanan zaben jarumi a Nollywood.

Lere Olayinka dai ya yamutsa hazo bayan ya wallafa hotunan bayanan rajistar zaɓen fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Emeka Ike.

Kara karanta wannan

Dan takarar sanata a NDC ya raba ƙafa tsakanin Obi da Tinubu

INEC ta gano yadda aka fitar da bayanan zabe daga ofishinta
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan yana bayani a ofishinsa da ke Abuja Hoto: INEC
Source: Twitter

Mai magana da yawun INEC, Mohammed Haruna, ya shaida wa Premium Times cewa binciken da hukumar tare da rundunar ‘yan sanda suka gudanar ya gano yadda bayanan suka fita daga na'urarta.

INEC ta yi bincike kan fitar bayanai

A karin bayanin da Mohammed Haruna ya yi wa jaridar, ya bayyana cewa wani jami’in zaɓe na karamar hukumar AMAC ne ya tura wa Olayinka waɗannan bayanai.

A cewar Haruna, binciken farko ya kai ga tsare mutane huɗu, daga ciki har da jami’an INEC uku da ‘yar wata jami’a guda.

Haka kuma, an kwace wayoyin hannu na wata jami’ar INEC da ‘yarta domin gudanar da cikakken bincike a kan bayyanar bayanan.

Yadda aka fitar da bayanai daga INEC

Hukumar ta bayyana cewa jami’ar INEC ɗin ce ta shiga shafin rajistar masu kaɗa kuri’a (CVR) ta duba bayanan Emeka Ike.

Bayan ta samu wadannan bayanai, sai ta tura su ga jami’in zaɓe na AMAC, wanda daga bisani ya aika wa Lere Olayinka. An kuma ce an yi amfani da wayar ‘yarta wajen ɗaukar hoton.

Kara karanta wannan

Bayan fama da doguwar jinya, fitaccen dilan man fetur a Kano, Audu Manager ya rasu

An gano jam'in INEC ne ya saci bayanai daga hukumar
Hadimin Wike, Lere Olayinka da ake zargi da karban bayanan sirri daga jami'in INEC Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

INEC ta ce wannan lamari ya jawo damuwa sosai a fannin tsaron bayanan masu kada kuri’a, musamman ganin cewa bayanan sun fito ne daga tsarin da ke hannun ma’aikatan da aka ba izini kawai.

Ya ce:

“Jami’in zaɓen na hannun ‘yan sanda kuma yana bayar da bayaninsa, wanda ya yi daidai da abin da aka samu daga bangaren Lere Olayinka cewa ba su ma san juna ba kafin wannan batu.”

Hukumar ta INEC ta sake tabbatar da cewa tsarin ta bai fuskanci kutse daga waje ba, sai dai amfani da damar aiki da wasu ma’aikata suka yi ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ci gaba da bincike.

INEC ta daukaka kara kan jadawalin zabe

A baya, kun samu labarin cewa hukumar INEC mai zaman kanta ta daukaka kara kan hukuncin da ya soke duka wa'adin da ta sanya wa jam'iyyun siyasa a jadawalin babban zaben 2027.

Lauyan INEC, Alex Izinyon (SAN), wanda ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara ta Abuja, ya nemi a jingine hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi a kan batun lokacin gudanar da zabukan.

A makon jiya ne, kotun tarayya ta soke wasu daga cikin tsare-tsaren INEC, daga cikin abubuwan da ta soke din har da wa'adin zaben fitar da gwani da na mika wa hukumar sunayen 'yan takara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng