Kwastam Ta Fitar da Sunayen Wadanda Suka Yi Nasara a Daukar Ma'aikatan 2024/2025

Kwastam Ta Fitar da Sunayen Wadanda Suka Yi Nasara a Daukar Ma'aikatan 2024/2025

  • Hukumar Kwastam ta Najeriya ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara a daukar ma'aikatan ASC II na shekarar 2024/2025
  • An umurci wadanda suka yi nasara su loda takardar shaidar lafiyarsu daga ranar 29 ga Yuli, 2026 cikin mako guda
  • Hukumar ta gargadi masu nasara cewa rashin bin umarnin da aka gindaya na iya jawo soke tayin aikin da aka ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja – Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da fitar da jerin sunayen karshe na wadanda suka yi nasara a aikin daukar ma'aikatan shekarar 2024/2025 domin nada su a matsayin Assistant Superintendent of Customs II (ASC II).

Sanarwar ta fito ne a ranar Litinin ta hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Maiwada, wanda ya bukaci duk wadanda suka nemi aikin su duba matsayin su ta shafin intanet na hukuma ko kuma ta wasu zababbun jaridun kasa.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta ana tsaka da garkuwa da mutane a hanyar Kano

Kwastam ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara a daukar ma'aikatan 2024/2025
Hukumar Kwastam ta gudanar da bita ga ma'aikatanta. Hoto: Nigeria Customs Service
Source: Facebook

Yadda za a tabbatar da samun aikin

Maiwada ya ce duk wadanda suka yi nasara za su samu sakon imel ko na wayar salula da ke dauke da umarnin mataki na gaba, in ji rahoton Punch.

Bayan samun sanarwar, an umurce su da su shiga shafin da hukumar ta tanada ta amfani da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) ko adireshin imel da suka yi rajista da shi domin loda takardar shaidar lafiyar jiki daga asibitin gwamnati da aka amince da shi.

A cewarsa, za a bude shafin da za a loda takardar lafiyar ne daga ranar Laraba, 29 ga Yuli, 2026, kuma dole ne a kammala aikin cikin mako guda.

Haka kuma an bukaci wadanda suka yi nasara su sabunta bayanin jihar da suke zaune a halin yanzu tare da amincewa da tayin aikin wucin gadi ta hanyar danna maballin "Accept Offer."

Za a sanar da ranar tantancewa

Maiwada ya bayyana cewa bayan kammala wadannan matakai, hukumar za ta aika wa wadanda suka yi nasara da lambar Trainee Identification Number cikin mako guda.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida, sojan da ake nema ruwa a jallo ya shigo hannu

Ya kara da cewa za a sanar da cikakkun bayanai kan tantance takardu da gwajin zahiri, ciki har da ranaku, wurare da abubuwan da ake bukata, ta hanyoyin sadarwa na hukuma.

Kwastam ta aika sako ga wadanda suka yi nasarar samun aiki a hukumar.
Shugaban hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, yana magana ga 'yan jarida. Hoto: Nigeria Customs Service
Source: Facebook

NCS ta gargadi wadanda suka yi nasara

Vanguard ta rahoto cewa hukumar ta gargadi duk wadanda sunayensu suka fito da su bi duk umarnin da aka bayar cikin wa'adin da aka kayyade.

Ta ce duk wanda ya gaza cika sharuddan ko ya kasa kammala matakan cikin lokacin da aka tanada na iya rasa damar aikin da aka ba shi.

A karshe, Maiwada ya ce Shugaban Hukumar Kwastam, a madadin Hukumar Gudanarwa ta NCS, ya taya duk wadanda suka yi nasara murna tare da bayyana fatan ganin sun fara aiki cikin kwarewa, gaskiya da hidima ga kasa.

Hana jami'an kwastam tu'ammali da kwaya

A wani labari, mun ruwaito cewa, kwastam ta shirya yaki da matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi daga wajen jami'an da ke aiki a karkashinta.

Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa ba za su lamunci ma'aikata na aiki a cikin yanayi mara kyau ba.

Ya bada umarnin gudanar da gwajin miyagun kwayoyi ga sababbin ma'aikata da wadanda ke bakin aiki a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com