Dan Takarar Sanata a NDC Ya Raba Kafa tsakanin Obi da Tinubu
- Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi gabanin zaɓen 2027
- Sai dai ya ce har yanzu yana goyon bayan wasu muhimman sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar
- Omo-Agege ya bayyana cewa yana ganin 'yan Najeriya za su fi amincewa da Peter Obi wajen aiwatar da irin waɗannan manufofi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Delta –Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ovie Omo-Agege, ya bayyana cewa zai mara wa Peter Obi baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sai dai ya bayyana cewa har yanzu yana goyon bayan wasu muhimman manufofin tattalin arziki da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bullo da su.

Source: Twitter
Omo-Agege ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin The Morning Show na gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba 3 ga watan Yuni, 2026.
Dan takarar sanata ya goyi bayan Obi
Jaridar Punch wallafa cewa da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya amince da Peter Obi bayan ya dade yana kare manufofin tattalin arzikin Shugaba Tinubu, Omo-Agege ya ce ra'ayinsa kan waɗannan manufofi bai canza ba.
Ya ce:
"Ni dan APC ne. Ban bar APC ba; jam'iyyar ce ta bar ni tare da magoya bayana sama da 230,000 a jihar Delta."
Dan takarar a NDC na son manufofin Tinubu
Tsohon sanatan Delta ta Tsakiya ya ce har yanzu yana da yakinin cewa wasu daga cikin manyan matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka na da muhimmanci.
Ya kara da cewa cire tallafin man fetur da kuma inganta farashin Naira muhimman sauye-sauye da suka zama wajibi.

Source: Facebook
Ya ce:
"Lokacin da shugaban kasa ya gabatar da manufofin tattalin arziki, musamman batun farashin Naira da cire tallafin mai, na goyi bayan su kuma har yanzu ina goyon bayansu."
Omo-Agege ya ce bai kamata a dauki waɗannan manufofi a matsayin mallakar APC ko Tinubu kaɗai ba.

Kara karanta wannan
Shugaban Obidients ya tabo batun 'rusa' masallacin Peter Obi lokacin da yake gwamna
Ya kara da cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar NDC ya dade yana goyon bayan irin waɗannan tsare-tsare da sauyin tattalin arziki da Bola Tinubu ya zo da su.
Ya bayyana cewa saboda haka zai ci gaba da martaba Tare da goyon bayan wadannan manufofi don cigaban ƙasa.
Omo Age ya samu takara a NDC
A baya, mun wallafa cewa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, ya sanar da matakin siyasa da zai dauka bayan ya fice daga APC.
Omo Agege, wanda daya ne daga cikin masu fada a ji na APC ya yi murabus daga jam'iyya mai mulki a wani sauyi na siyasar jihar Delta bayan sabani a jihar.
Bayan tsohon Mataimakin shugaban majalisar ya fadi dalilinsa na barin APC, NDC ta yi nasa tukwici bisa abin da ta kira kwarewarsa a aiki, an ba shi takarar sanata
Asali: Legit.ng
