Ukraine Ta Tsokano Iran, Tehran za Ta kai Mata Farmakin Ramuwar Gayya
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce harin da Ukraine ta kai wa wani jirgin kasuwancin Iran a Tekun Caspian ba zai wuce ba tare da martani ba
- Iran ta zargi Isra'ila da ingiza harin, yayin da Ukraine ta ce ta kai hari ne kan jirgin ruwan yaƙin Rasha da jiragen da ke ɗauke da kayan sojin da ke da alaƙa da Iran
- Tehran ta gayyaci jami'in diflomasiyyar Ukraine domin nuna rashin amincewa da abin da ta kira "aikin ta'addanci" da aka aikata a kan jirginta a cikin teku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Gwamnatin Iran ta yi gargaɗin cewa ba za ta ƙyale harin da Ukraine ta kai wa wani jirgin kasuwancinta a Tekun Caspian ba, tana mai cewa za ta ɗauki matakin da ya dace.
Hakan na zuwa ne yayin da lamura suka dan lafa a Gabas ta Tsakiya bayan Amurka ta sanar da dakatar da kai hare-hare kan Iran.

Source: Getty Images
Al Jazeera ta rahoto cewa Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar Lahadi, inda ya ce harin ya saɓa wa kundin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ukraine: Iran ta zargi Isra'ila
Araghchi ya zargi Isra'ila da ƙoƙarin jawo ƙasashen Turai cikin rikicin da ake yi a yankin ta hanyar ingiza harin.
Ya bayyana cewa ya tattauna batun da babbar jami'ar harkokin wajen Tarayyar Turai, Kaja Kallas, da kuma Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce harin da aka kai ranar Asabar ya haddasa fashewar jirgin kasuwancin Iran, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani ma'aikacin jirgin tare da jikkata wasu da dama.
Sai dai Ukraine ta ce harin nata ya nufi wani jirgin ruwan yaƙin Rasha da kuma wasu jiragen da ake zargin suna jigilar kayan aikin soja masu alaƙa da Iran.
Bugu da kari, Iran ta dage cewa ba ta taɓa shiga rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ba.
Iran za ta farmaki Ukraine
Shugaban Kwamitin Tsaro da Harkokin Wajen Majalisar Dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya ce Ukraine za ta iya fuskantar martani kan harin.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Azizi ya ce:
"Duk wani hari da aka kai wa Iran zai fuskanci martani, kuma Ukraine ma za ta fahimci cewa Iran ba ta barin irin waɗannan hare-hare su wuce ba tare da martani ba."
Haka kuma Iran ta gayyaci jami'in diflomasiyyar Ukraine da ke Tehran domin nuna rashin amincewarta da abin da ta kira mugun aiki da ya saɓa wa doka.

Source: Getty Images
Magana kan makaman Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya musanta rahotannin da ke cewa hare-haren da Amurka ke kaiwa sun rage mata yawan makaman yaƙi.
A bayanin da ya yi, shugaba Trump ya ce Amurka tana da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya, kuma fiye da adadin da take buƙata.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa jami'an Pentagon na sa ido kan adadin makaman kariya daga hare-haren sama da ake da su, domin tabbatar da cewa ba su ƙare ba.
Asali: Legit.ng

