'Tinubu Ya Gaji': Obi Ya Ce Matsalolin Najeriya Sun fi Karfin Tinubu
- 'Dan takarar shugaban 'kasa, Peter Obi ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara game da takarar a babban zaben 2027 mai zuwa a cikin yan watanni
- Obi, wanda ke takarar tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba da shawarar ne domin a cewar shugaba Tinubu ya gaji kuma ba shi da isasshen ƙarfi a jikinsa
- Obi ya ce talauci, yunwa da rashin tsaro na ƙara ta'azzara, yana kira ga shugabanci mai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwar talakawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ajiye shugabanci kafin zaɓen 2027.
Ya ce ya bayar da wannan shawara ne saboda a cewarsa, shugaban ya gaji kuma ba shi da ƙarfin da ake buƙata domin magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaron da ke addabar Najeriya.

Source: Facebook
Peter Obi ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na Channels Television a karshen mako.
Shawarar Obi ga Tinubu game da 2027
A ruwayar The Cable, Obi ya ce duk da cewa Tinubu ya yi ayyuka masu kyau a lokacin da yake gwamnan jihar Legas, irin wannan kuzari da jagoranci ba su bayyana a mulkinsa na shugaban ƙasa ba.
Obi ya ce:
"Tinubu na lokacin gwamna ba shi ne Tinubu na yau ba. Ya gaji, kuma ya kamata a bar shi ya yi ritaya cikin kwanciyar hankali."
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa Najeriya tana tafiya a hanya mara kyau, kuma tana buƙatar shugaba mai kuzari da jajircewa domin sauya alkiblar ƙasar.
Obi ya gano matsalolin Najeriya
Ya ƙara da cewa gwamnatin yanzu ba ta kawo mafita ga matsalolin da suka haɗa da talauci, yunwa, rashin tsaro da kuma gazawar shugabanci ba.
A cewarsa, rahotannin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun nuna girman matsalolin Najeriya, amma maimakon a tattauna hanyoyin magance su, 'yan siyasa sun fi mayar da hankali kan mutane da siyasa.

Source: Facebook
Ya yi nuni da rahoton Bankin Duniya wanda ya ce kusan 79% na ’yan Najeriya na iya fadawa cikin talauci. Haka kuma ya ce ya kamata a fi tattauna matsalar yara da ba sa zuwa makaranta, harkokin lafiya da yadda ake amfani da kuɗin gwamnati yadda ya kamata.
Peter Obi ya kara da cewa kamata ya yi shugaban ya yi ritaya, ya koma gida ya ci gaba da kula da kansa a cikin kwanciyar hankali.
Tinubu ya yi magana kan ci gaban kasa
A baya, mun kawo labarin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a fannonin tsaro, ilimi, ababen more rayuwa da tattalin arziki domin gina Najeriya mai ɗorewa.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa fiye da ɗalibai miliyan ɗaya sun amfana da shirin bashin karatu na NELFUND, yayin da aka inganta manyan cibiyoyin ilimi da zai inganta rayuwar matasa a dukkanin jihohin kasar.
Bola Ahmed Tinubu ya kara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da manyan ayyukan hanyoyi, layukan dogo da wutar lantarki domin bunƙasa tattalin arziki da haɗa sassan ƙasar ta hanyar sufuri mai sauki.
Asali: Legit.ng

