INEC: 'Yan Sanda Sun Yi wa Hadimin Wike Tambayoyi kan Fitar Bayanan Masu Zabe

INEC: 'Yan Sanda Sun Yi wa Hadimin Wike Tambayoyi kan Fitar Bayanan Masu Zabe

  • An yi wa hadimin Nyesom Wike, Lere Olayinka tambayoyi a hannun ‘yan sanda kan fitar da bayanan masu kada kuri’a daga shafin hukumar zabe ta kasa (INEC)
  • Masu bincike daga sashen leken asiri na rundunar ‘yan sanda sun yi wa Lere Olayinka tambayoyi a ranar Talata a hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Abuja
  • Wannan tambayoyin wani bangare ne na bincike kan laifin yanar gizo, amfani da ma’ajiyar bayanai ba tare da izini ba, da kuma fitar da takardun sirri na kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jami’an bincike na 'yan sanda sun yi wa babban hadimi ga Ministan birnin tarayya, Lere Olayinka, tambayoyi tare da tsare wani jami’in INEC kan zargin fitar da bayanan rajistar mai kada kuri’a ba tare da izini ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace yayar tsohon ministan Tinubu da 'ya'yanta tagwaye

Majiyoyin ‘yan sanda, wadanda suka yi magana bisa sharadin a sakaya sunayensu domin ba su da izinin yin magana a bainar jama’a, sun ce binciken ya samo asali ne daga wani korafi da aka shigar.

Lere Olayinka a Abuja
Hadimin Nyesom Wike, Lere Olayinka a wajen wani taro. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Bincike da ake yi kan bayanan INEC

Punch ta ce jami’in INEC da aka tsare na fuskantar bincike ne kan zargin fitar da bayanan sirri na rajistar masu kada kuri’a da suka shafi wata takaddamar siyasa da ta taso yayin zaben fitar da gwani na wata jam’iyya.

“Muna tsare da jami’in INEC na AMAC a Abuja tun jiya.
“Haka kuma, an gayyaci Lere Olayinka, kuma an yi masa tambayoyi kan lamarin Emeka Ike."

INEC: Bayanin hadimin Nyesom Wike

The Cable ta wallafa cewa, a cikin bayaninsa, Lere Olayinka ya amsa cewa ya wallafa bidiyon zanga-zangar siyasar da aka yi a ofishin AMAC a shafukansa na sada zumunta.

“Ya bayyana cewa jami’in zaben na AMAC, wanda bai taba saninsa ba a baya, ya tuntube shi ta Facebook domin bayyana fushinsa cewa ana yi wa INEC barazana da zanga-zangar wasu mutane da ba ma halastattun masu rajistar zabe ba ne a Abuja.

Kara karanta wannan

Buratai ya yi tone tone kan 'yan siyasa game da rashin tsaron Najeriya

“Olayinka ya amsa cewa jami’in INEC ya yi alkawarin aiko masa da hujjar katin zabe na wucin gadi, wanda daga bisani aka aiko masa ta WhatsApp.”

Majiyar ta ce daga baya jami’in zaben ya goge wasu sassan tattaunawar da suka yi ta WhatsApp bayan takardar da aka fitar ta haifar da ce-ce-ku-ce a bainar jama’a.

“Binciken kwararru ya sake gano sakonnin da aka goge,”

In ji majiyar.

Shugaban INEC, Farfesa Amupitan
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Joash Amupitan na bayani a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Yayin da jami’in zaben ke ci gaba da zama a tsare, majiyar ta ce an ba Olayinka beli bayan an yi masa tambayoyi. Da aka tuntube shi, Olayinka ya tabbatar da cewa an gayyace shi kuma ya amsa gayyatar.

Jam’iyyun sun cika sharudan INEC

A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar INEC ta sanar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa 22 da aka yi wa rajista a Najeriya sun yi nasarar mika rajistar mambobinsu.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, hukumar ta ce an kammala karbar rajistar ne bayan an bai wa jam’iyyun siyasa karin lokaci sakamakon damuwar da aka nuna kan wa’adin farko.

A cewar INEC, karin lokacin ya biyo bayan wani taro da aka gudanar tare da jam’iyyun siyasa a ranar 24 ga Maris, 2026, inda masu ruwa da tsaki suka nuna damuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng