Iran Ta Gano Kasashen da ke Taimakon Amurka a Yakin da Suka Yi

Iran Ta Gano Kasashen da ke Taimakon Amurka a Yakin da Suka Yi

  • Iran ta zargi wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya da taimaka wa Amurka wajen kai hare-haren soji a kan ƙasarta
  • Gwamnatin Tehran ta ce wasu ƙasashen sun ba dakarun Amurka damar amfani da yankunansu wajen kai hare-hare
  • Sai dai Iran ta jaddada cewa har yanzu tana son kyakkyawar alaƙa da maƙwabtanta duk da zarge-zargen da ta yi a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran, Iran – Gwamnatin Iran ta zargi wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya da taimaka wa Amurka wajen kai hare-haren soji a kanta.

Iran ra ta yi magana tana mai cewa sun ba dakarun Amurka damar amfani da yankunansu wajen kai hare-haren a yakin da suka yi.

Abbas Araghchi a Iran
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta rahoto cewa kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya yi wannan zargi ne yayin taron manema labarai na mako-mako da aka gudanar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ukraine ta tsokano Iran, Tehran za ta kai mata farmakin ramuwar gayya

Kasashen da Iran ta zarga

Baqaei ya ce Iran tana ɗora wa Amurka alhakin hare-haren da aka fara kai mata tun ranar 28 ga Fabrairu, amma ba za ta iya yin shiru kan rawar da wasu ƙasashen yankin suka taka ba.

A News ta rahoto ya ce:

"Ba za mu iya yin watsi da yadda wasu ƙasashen yankin suka shiga cikin wannan hari ba."

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ƙasashen sun ba Amurka damar amfani da yankunansu wajen kai hare-hare kan Iran, kuma a wasu lokutan ma sun shiga kai tsaye cikin harin.

Iran na son zaman lafiya

Duk da zarge-zargen, Baqaei ya jaddada cewa Iran ba ta da wata ƙiyayya ga maƙwabtanta, kuma tana son kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa tsakaninta da ƙasashen yankin.

Ya ce akwai dangantaka mai ƙarfi da muradun bai ɗaya tsakanin Iran da ƙasashen yankin Tekun Fasha, waɗanda za su iya zama tubalin gina amincewa da haɗin kai.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara fuskantar matsalar makamai, Trump ya dakatar da hare hare kan Iran

Mojtaba Khamenei a Iran
Jagoran kasar Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai ƙasashen yankin Tekun Fasha sun sha musanta zargin cewa sun taimaka wa Amurka wajen kai hare-hare kan Iran, suna kuma zargin Tehran da kai hare-hare kan cibiyoyin fararen hula a yankunansu.

Iran ta kira jakadan Faransa

A daya bangaren kuma, Iran ta gayyaci jakadan Faransa domin nuna rashin jin daɗinta kan abin da ta kira katsalandan cikin harkokinta.

Hakan ya biyo bayan zargin da Tehran ta yi cewa jami'an diflomasiyyar Faransa biyu sun gudanar da ayyuka da sunan hulɗa da ƙungiyoyin farar hula kafin jami'an tsaro su tsare su na ɗan lokaci a ranar 19 ga Yulin 2026.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce gwamnatin Faransa ta daina abin da ya kira tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Iran ta hanyar amfani da wasu hujjoji marasa tushe.

Martanin Iran ga Ukraine

A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta bayyana cewa za ta mayar da martani kan harin da Ukraine ta kai wa wani jirgin ruwan kasuwancinta a Tekun Caspian.

Kara karanta wannan

An ja daga tsakanin Amurka da China kan haraji, kasar ta gargadi Trump

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, Esmaeil Baqaei, ya ce Iran ba za ta yi shiru ba kan harin, yana mai jaddada cewa kare tsaron ƙasa da martabarta ne zai kasance a gaba.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an Iran na nazarin irin matakin da za su ɗauka, ciki har da yiwuwar ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Rasha ko kuma ɗaukar wasu matakan soji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng