Bayan Fama da Doguwar Jinya, Fitaccen Dilan Man Fetur a Kano, Audu Manager Ya Rasu
- Shahararren ɗan kasuwar man fetur da gidaje na Kano, Alhaji Abdullahi Ahmad ya koma ga Mahaliccinsa bayan babbar sallar nan
- Fitaccen ɗan kasuwar da aka fi sani da Audu Manager ya rasu a safiyar Laraba 3 ga watan Yuni, 2026 bayan ya sha fama da doguwar rashin lafiya
- Ya rasu a asibitin Saudi German da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar bayan nan kuma an bayyana yadda za a a birne shi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shahararren ɗan kasuwar man fetur kuma mai zuba jari a harkokin gidaje, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manager, ya rasu yana da shekaru 68 a duniya.
Audu Manager ya rasu a safiyar ranar Laraba, 3 ga watan Yuni, 2026 a Asibitin Saudi German da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

Source: Facebook
Ɗansa, Surajo Audu Manager, ne ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa ga jaridar Daily Nigerian, inda ya bayyana cewa iyalan mamacin na ci gaba da shirye-shiryen dawo da gawarsa Kano domin yi masa jana'iza.
Shirye-shiryen jana'izar Audu Manager
Surajo ya bayyana cewa an tsara gudanar da sallar jana'izar marigayin a Masallacin Jami’ur Rahma Juma’at da ke Kano bayan sallar Juma'a.
Sai dai ya ce idan aka samu jinkiri wajen isowar gawar daga Masar, za a gudanar da jana'izar ne bayan sallar La'asar.

Source: Original
Ya ce:
"Za a yi sallar jana'izar sa a Masallacin Jami’ur Rahma Juma’at da ke Kano bayan sallar Juma'a. Amma idan aka samu jinkirin isowar gawar, za a yi jana'izar bayan sallar La'asar."
Rasuwar Audu Manager ta jefa iyalai, abokai da masu hulɗa da shi cikin jimami, musamman ganin yadda ya shahara a harkokin kasuwanci a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Yadda Audu Manager ya shahara a kasuwanci
Marigayi Audu Manager ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan kasuwa a fannin man fetur a Najeriya, musamman a ɓangaren kasuwancin man fetur na ƙasa.
Ya mallaki jerin gidajen mai a sassa daban-daban na ƙasar nan, lamarin da ya sanya ya zama sanannen suna a masana'antar makamashi.
Baya ga harkar man fetur, marigayin ya yi manyan zuba jari a fannin gidaje, noma da sauran sana'o'i daban-daban da suka taimaka wajen samar da ayyukan yi ga jama'a.
Wadanda suka san shi sun bayyana shi a matsayin mutum mai hangen nesa da jajircewa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci.
Audu Manager ya rasu ya bar matansa, 'ya'yansa da sauran manyan iyalai da dama. Ana sa ran ɗaruruwan mutane daga sassa daban-daban za su halarci jana'izarsa.
Fitaccen dan siyasa ya rasu a Kano
A bara, mun kawo labarin cewa an shiga alhini a jihar Kano bayan rasuwar fitaccen dan siyasa, Ahmadu Haruna Zago, wanda aka fi sani da Ɗanzago, bayan ya sha fama da jinya.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi jana'izarsa a gidansa da ke Kurna Tudun Bojuwa da misalin karfe 1:00 na ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu, 2025 inda ƴan uwa da abokai suka halarta.
Kafin rasuwarsa, Ɗanzago ya rike mukamin shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano (REMASAB) a bangaren tsaftar muhalli kuma fitaccen ɗan siyasa ne da ya dade a harkar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


