2027: Tinubu Zai Samu Gagarumar Nasara a Arewa, Inji Jigon APC a Jihar Kano

2027: Tinubu Zai Samu Gagarumar Nasara a Arewa, Inji Jigon APC a Jihar Kano

  • Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce ayyukan ci gaba da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa a Arewa za su tabbatar masa da nasara a 2027
  • Jigon APC ya lissafo manyan ayyukan Tinubu da suka hada da tituna, layin dogo, bututun iskar gas da noma da ke gudana a jihohin Arewa
  • Ya ce dimbin ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke yi sun kara karfafa goyon bayan al’umma ga Shugaba Tinubu a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a jihohin Arewa a zaben shugaban kasa na 2027.

Kwankwaso ya danganta wannan hasashe da dimbin ayyukan raya kasa da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa a yankin Arewa, wadanda ya ce kudinsu ya kai tiriliyoyin naira.

Kara karanta wannan

'Ba mu da zabi': Nyesom Wike ya yi magana kan sake zaben Tinubu a 2027

Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce Tinubu zai samu gagarumar nasara a Arewa a 2027.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wani gangamin jam'iyyar APC. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Arewa za ta ba Tinubu kuri'u a 2027

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano, ya ce nasarar sake zaben shugaban kasar ta kusa zama tabbatacciya saboda irin goyon bayan da yake samu daga al’ummar yankin, in ji rahoton Tribune.

“Shugaba Tinubu zai iya kwanciya da idanunsa biyu a rufe domin batun sake zabensa kusan ya tabbata. Arewa gaba daya, musamman Kano, za ta ba shi kuri’u masu yawa da za su tabbatar masa da nasara cikin sauki a 2027,” in ji shi.

Musa Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kaddamar da manyan ayyukan tituna da ke da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da sufuri a yankin Arewa.

Ayyukan Tinubu a Arewacin Najeriya

Daga cikin ayyukan da ya ambata akwai aikin titin Kano zuwa Kongolom mai tsawon kilomita 132, wanda aka ware masa sama da Naira biliyan 334.

Ya ce aikin zai kara hada jihohin Kano, Jigawa da Katsina tare da saukaka zirga-zirgar jama'a da kasuwanci.

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Hakazalika, ya yaba da aikin sake gina hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano, wanda ake yi da sabuwar fasahar siminti mai karfi tare da karin matakan tsaro.

Jigon na APC ya kuma yi tsokaci kan aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1,068, in ji rahoton Punch.

A cewarsa, titin mai layuka shida da kuma layin dogo da aka tsara a cikinsa zai taimaka wajen bunkasa hada-hadar kasuwanci da hada yankuna daban-daban na Najeriya.

Ci gaba a bangaren layin dogo

Kwankwaso ya ce aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar na daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.

Ya bayyana cewa layin dogon mai tsawon kilomita 284 zai saukaka safarar kayayyaki da karfafa kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar. Aikin ya ratsa jihohin Kano, Jigawa da Katsina.

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya kan yadda ake ci gaba da aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Abuja–Kaduna–Kano (AKK).

Kwankwaso ya ce aikin mai tsawon kilomita 614 zai taimaka wajen bunkasa masana’antu, samar da karin wutar lantarki da kuma inganta amfani da iskar gas a Arewa.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Musa Iliyasu Kwankwaso ya zayyano ayyukan Tinubu a Arewacin Najeriya.
Musa Iliyasu Kwankwaso da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Inganta harkar lafiya

Kwankwaso ya ce gwamnatin Tinubu ta kuma mayar da hankali wajen inganta cibiyoyin lafiya a yankin Arewa.

Ya ce ana ci gaba da inganta asibitocin koyarwa na gwamnatin tarayya tare da farfado da dubban cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta hanyar shirin IMPACT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com