'Sheɗanci ne Kin Goyon bayan Tinubu': Gwamna Ya Kausasa Harshe kan Zaben 2027
- Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi magana game da salon mulkin Bola Tinubu a Najeriya da sauye-sauyen tattalin arziki
- Oborevwori ya ce zai zama rashin adalci ga al’ummar Delta su kada kuri’a ga wani 'dan takara ba Shugaba Bola Tinubu ba a zaɓen 2027
- Ya bayyana cewa matar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, tana da asali ta uwa daga Itsekiri na Warri, abin da ya sa Tinubu ya zama suruki ga jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana goyon bayansa dari bisa dari ga shugaba Bola Tinubu na Najeriya.
Oborevwori ya bayyana cewa zai zama abin da bai dace ba ga mazauna jihar su kada kuri’ar kin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan
"Rashin zaben Tinubu na iya zama zunubi," Gwamnan Delta ya ja hankalin 'Yan Najeriya

Source: Twitter
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Arise TV ranar Talata, 2 ga Yuni, 2026.
Alakar matar Bola Tinubu da jihar Delta
Gwamnan ya ce Tinubu ne kaɗai daga cikin manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa da ke da alaƙa kai tsaye da Delta.
Oborevwori ya bayyana cewa matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tana da asalin uwa daga kabilar Itsekiri ta Warri, abin da ya sa shugaban ƙasar ya zama suruki ga jihar.
Ya ce:
“Daga cikin ‘yan takarar da suka fito, Bola Ahmed Tinubu ne kaɗai ke da alaƙa da Delta, shi surukinmu ne, kuma zai zama abin da bai dace ba a yi wa surukinmu adawa.”

Source: Twitter
Gwamnan ya ƙara da cewa mutanen Delta da sauran yankin Kudu maso Kudu yanzu sun fahimci muhimmancin goyon bayan wanda suke kallon nasu ne, bayan yaudarar siyasa da suka ce sun fuskanta a baya.
Gwamna ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu
Ya bayyana cewa kasancewar uwargidan shugaban ƙasa tana da ƙarfi da karɓuwa a jihar ya ƙara tabbatar da goyon bayan Tinubu musamman a tsakanin al’ummar Itsekiri.
A cewarsa, kasancewarsa ɗan kabilar Urhobo kuma gwamnan jihar na taimakawa wajen samun goyon bayan sauran ƙabilu ga gwamnatin tarayya da shugabanta, cewar Vanguard.
Baya ga batun alaƙar dangi, Oborevwori ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana cewa sun fara samar da sakamako mai anfani ga jihar Delta.
Ya ce yawan kuɗaɗen shiga da jihar ke samu a yanzu, waɗanda ake amfani da su wajen ayyukan gine-gine da raya ƙasa, sun samo asali ne daga manufofin gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya jaddada cewa da ba a aiwatar da waɗannan gyare-gyaren tattalin arziki ba, da jihohi ba za su samu isassun kuɗaɗen gudanar da manyan ayyuka da inganta rayuwar jama’a ba.
Gwamna ya magantu kan kudin shiga a Delta
A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi tsokaci kan kudaden da ake ba gwamnoni daga asusun tarayya.
Sheriff Oborevwori ya bayyana cewa abin da gwamnoni ke karba duk karshen wata ya karu sosai fiye da wanda suke samu a baya.
Gwamnan ya bayyana cewa masu cewa babu kudi a kasar nan, ba gaskiya suke gayawa 'yan Najeriya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

