Sabuwar Rigima: Atiku da Wike na Musayar Yawu kan Zaben 2027
- 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ragargaji Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike kan zaben 2027
- Atiku Abubakar ya ce masu kada kuri’a a jihar Rivers suna da wayewar kai da za su iya yanke hukuncin wanda zai yi nasara a zabukan jihar
- Hakan na zuwa ne bayan da Wike ya yi alkawarin cewa Atiku ba zai samu kashi 10 cikin 100 na jimillar kuri’un da za a kada a jihar Rivers ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya caccaki Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan kalamansa na baya-bayan nan a kan kuri'un jihar Rivers.
Hakan na zuwa ne bayan Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na ADC, yayin da Wike ya sha alwashin tabbatar da nasarar Tinubu a 2027.

Source: Facebook
Abin da Wike ya fadawa Atiku
Punch ta ce tsohon gwamnan jihar Rivers ya bayyana cewa Atiku da ADC ba za su samu kashi 10 cikin 100 na jimillar kuri’un da za a kada a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 a jihar da ke Kudu maso Kudu ba.
Wike ya bayyana hakan ne a wata liyafar cin abinci da aka shirya a ranar Lahadi domin karrama ’yan takarar kungiyar Rainbow Coalition na zaben shekarar 2027 a jihar.
A cewarsa, babu wani dan takara daga wata jam’iyya da zai lashe zaben gwamna a shekarar 2027 sai wanda kungiyar Rainbow Coalition ta amince da shi.
Martanin Atiku ga Wike
Da yake mayar da martani tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce masu kada kuri’a a jihar Rivers suna da hikima da wayewar kai da za su iya yanke hukuncin sakamakon zabukan jihar.
Leadership ta wallafa cewa Atiku ya mayar da martani ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Litinin.
Atiku ya ce babu wani mutum, komai tasirinsa ko kusancinsa da Gwamnatin tarayya, da zai iya tsara yadda daukacin wata jiha za ta kada kuri’a.
Ya kara da cewa kalaman ministan sun nuna yadda fargaba ke kara kama sansanin Tinubu sakamakon bullowar wata hadakar adawa mai karfi karkashin ADC.
Atiku ya ce abin dariya ne kuma abin damuwa yadda Wike yanzu yake magana kamar kuri’un jihar Rivers mallakarsa ne da zai raba yadda ya ga dama.
“Kuri’un Rivers ba mallakarka ba ne. Mutanen Jihar Rivers ba bayi ne na siyasa ba. Su ’yan Najeriya ne masu hankali da ’yanci, za su yi zabe bisa ga lura halin da suke ciki da kuma irin makomar da suke so ga ’ya’yansu."

Source: Facebook
Atiku ya tattauna da Amaechi
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi cikakken bayani kan ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi.
Atiku ya ce tattaunawarsu ta mayar da hankali ne kan kalubalen tattalin arziki da matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta da kuma bukatar samar da mafita.
'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya bayyana hakan ne a wani sako a makon da ya wuce bayan ya kai wa Amaechi ziyara a gidansa da ke Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

