Ana Zargin Gwamna Oyo da Shirya Sace Dalibai don Bata Sunan Tinubu

Ana Zargin Gwamna Oyo da Shirya Sace Dalibai don Bata Sunan Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi zargin cewa an shirya sace ɗalibai da malamai a wasu makarantun jihar Oyo ne da gan-gan
  • Ya yi zargin cewa gwamnatin Gwamna Seyi Makinde ce ta shirya sace su a matsayin wani yunƙuri na ƙoƙarin bata sunan Bola Ahmed Tinubu
  • Fayose ya ce ba a yin adalci wajen zargin shugaban kasa da matsalolin tsaro, alhali gwamnatocin jihohi ya kamata a rika jefa wa tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi zargin cewa gwamnatin Jihar Oyo ce ta shirya sace ɗalibai da malamai a sassa daban-daban na jihar a matsayin wani shiri na kunyata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Sace daliban ya jawo suka ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu, wasu na cewa ya gaza kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Jam'iyyar APC ta bukaci Gwamna Seyi Makinde ya yi murabus

Ayo Fayose da Bola Tinubu
Ayo Fayose yana gaisawa da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Fayose ya yi wannan zargin ne a hira da Channels TV, inda ya soki yadda gwamnatin Oyo ta tunkari lamarin, yana mai cewa akwai alamun dalilan siyasa sun yi tasiri a yadda aka tafiyar da lamarin.

Rashin tsaro: Fayoye ya kare gwamnatin Tinubu

Da yake mayar da martani, Fayose ya ce gwamnatocin jihohi ne ke da babban alhakin tsaron cikin gida, kuma bai kamata su rika zargin gwamnatin tarayya kai tsaye ba.

“Bari na tsaya a jihar Oyo, kafin ka kai ga shugaban ƙasa a tsarin shugabanci, akwai ƙaramar hukuma, akwai jiha, kuma jiha na da kuɗin tsaro da kuma mutane da ya kamata su yi aiki,”

In ji shi.

Fayose ya ce Gwamna Seyi Makinde bai mayar da martani cikin gaggawa ba, yana zargin cewa ya fi mayar da hankali kan harkokin siyasa fiye da magance matsalar.

Vanguard ta rahoto ya ce:

“A Jihar Oyo, na yi imani—duk da cewa zan iya yin kuskure—amma wani lokaci ana iya shirya irin wannan abu. Gwamnan Oyo yana wajen siyasa da ‘yan takararsa a lokacin da wannan sace-sacen ya faru,”

Kara karanta wannan

Gwamna ya ajiye girma yana rokon talaka afuwa da sake zaben APC a 2027

“Bai ɗauki wani mataki nan da nan ba, babu wani gaggawa da aka yi, sai bayan taron siyasa ne ya je ya ziyarci iyalan waɗanda abin ya shafa.”
Masu zanga-zangar sace dalibai a Oyo.
Yadda matasa suka yi zanga-zangar sace dalibai a Oyo. Hoto: Take It Back Movement
Source: Facebook

Zargin bata wa Tinubu suna

Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa an shirya lamarin ne domin ɓata sunan gwamnatin tarayya da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.

“Wani lokaci ina ganin cewa sace ɗaliban makarantar Oyo gwamnatin Jihar Oyo ce ta shirya domin bata sunan Shugaba Tinubu,”

In ji Fayose.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, gwamnatin Jihar Oyo ko Gwamna Seyi Makinde ba su mayar da martani kan wannan zargi ba.

NUT ta fara zanga-zanga

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar NUT ta sanar da gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya a faɗin ƙasa domin jawo hankali kan sace malamai da ɗalibai a Oyo.

Da yake magana a ranar Litinin, shugaban ƙungiyar, Audu Titus Amba, ya ce NUT na cikin damuwa sosai tana jiran ganin an sako waɗanda aka sace lafiya.

Amba ya nuna damuwa kan yadda ‘yan ta’adda ke amfani da waɗanda suka sace don neman kudin fansa, lamarin da ya ce yana kawo cikas ga ƙoƙarin ceto su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng