Yan Najeriya Sun Dura kan Wike bayan Izgili ga Ubangiji game da Inganta Abuja
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce gwamnati ba za ta janye shirin sake fasalin wurin shakatawar Jabi ba duk da korafin Fasto Sarah Omakwu
- Wike ya ce tsofaffin masu kula da wurin sun mayar da yankin wurin kazanta da wuraren da ka iya zama mafakar masu laifi a birnin Abuja
- Ya jaddada cewa gwamnati za ta bai wa sababbin masu zuba jari filin tare da sharadin ci gaba cikin lokaci ko kuma a sake kwace shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya kare matakin gwamnatin tarayya na sake fasalin wurin shakatawa da ke Jabi a Abuja domin inganta shi.
Tun a watan Fabrairun 2026, Hukumar Birnin Tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da wasu kamfanoni biyu domin mayar da wurin cibiyar yawon bude ido da nishadi.

Kara karanta wannan
Wike vs Turaki: 'An ruguza yunkurin hana PDP tsaida dan takarar shugaban Kasa a zaben 2027'

Source: Twitter
Fasto ta roki Nyesom Wike alfarma
Babbar faston cocin 'Family Worship Centre' da ke Abuja, Sarah Omakwu, ta bukaci Wike da kada ya bai wa masu zaman kansu filin domin gine-gine, cewar TheCable.
Sarah ta bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ta wallafa a Instagram inda aka gan ta durkushe tana rokon ministan da kada a karbe wurin daga jama’a.
Da yake mayar da martani yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, Wike ya ce ba zai bari rokon na ta ya hana gwamnati aiwatar da abin da ya dace ba.
Ya ce an bai wa wani kamfani filin a baya domin bunkasa wurin zuwa cibiyar nishadi, amma daga baya wurin ya rikide zuwa shantaye marasa tsari.
Wike ya ce:
“Na je wurin wata rana na ga ba zai yiwu ba. Akwai otel amma wurin ya cika da shantaye, har mutum ba zai san ko masu laifi na boye a wurin ba."
Ministan ya bayyana cewa gwamnati ta kwace filin daga hannun wadanda suka gaza bunkasa shi, kuma yanzu za a bai wa masu zuba jari.

Source: Facebook
Izgilin Wike da ya jawo magana
Ya kara da cewa za a sanya sharudda masu tsauri ga sababbin masu kula da wurin, inda gwamnati za ta sake kwace filin idan ba a aiwatar da aikin cikin lokacin da aka kayyade ba.
Wike ya kuma yi watsi da rokon faston, yana mai cewa ko ta kira Ubangiji ya sauko, gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da shirin domin amfanin jama’a baki daya.
A cewarsa, gwamnati ba ta hana jama’a anfani da wurin ba, illa dai tana kokarin tabbatar da cewa an bunkasa yankin yadda ya dace domin ci gaban Abuja.
Kalaman minsitan sun jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya yayin yan kasar ke ganin saka Ubangiji a cikin lamarin bai dace ba, cewar Punch.
'Yan Najeriya da dama sun caccaki Wike kan yadda ya ke wasa da Ubangiji tare da gargadinsa cewa ya jira karshensa.
Rivers: Wike ya musanta tsayar da dan takara
An ji cewa Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi karin haske game da batun fitar da dan takara ko goyon bayansa a jihar Rivers.
Wike ya ce bai goyi bayan kowa ya shiga takarar gwamnan Rivers ta 2027 ba, yana jiran hadakar PDP da APC ta yanke matsaya.
Ya bayyana cewa ba su aiki tare da Gwamna Siminalayi Fubara, har yana zarginsa da karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

