‘Ba Mu da Zabi’: Nyesom Wike Ya Yi Magana kan Sake Zaben Tinubu a 2027
- Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana game da sake zaben Bola Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara
- Wike ya ce Rivers ba ta da wani zaɓi illa ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 domin samar da ci gaba
- Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta bai wa Rivers muƙamai da ayyukan ci gaba fiye da gwamnatocin baya, yana mai kira ga jama'a su yaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya nuna goyon bayansa ga nasarar Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Wike ya bayyana cewa Rivers ba ta da wani zaɓi face ta ci gaba da mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake samun nasara a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Wike ya yi wannan jawabi ne a Port Harcourt yayin wani taron cin abinci da 'Rainbow Coalition' ta shirya domin girmama ƴan takarar gwamna, majalisun tarayya da na jiha, cewar Channels TV.
Alfanun da Rivers ta samu a gwamnatin Tinubu
Tsohon gwamnan Rivers ya bukaci al'ummar jihar su kwatanta ribar da suka samu ƙarƙashin gwamnatin Tinubu da abin da suka samu daga gwamnatocin baya.
A cewarsa, daga shekarar 2023 zuwa yanzu, Rivers ta samu muƙamai da damammaki masu yawa, saboda haka ya kamata jama'a su nuna godiya ga shugaban ƙasa.
Wike ya ce siyasar ƙabila ko yanki bai kamata ta zama abin dubawa ba, yana mai jaddada cewa ci gaba da kyakkyawan shugabanci su ne mafi muhimmanci.
Ya kuma gargadi magoya baya cewa talbijin ba ya kawo ƙuri'u, yana mai cewa nasara tana fitowa ne daga aiki a rumfunan zaɓe, gundumomi da ƙananan hukumomi.

Source: Facebook
Gargadin da Wike ya yi a Rivers
Ministan ya nuna ƙwarin gwiwa cewa 'Rainbow Coalition' za ta mamaye zaɓukan gaba a Rivers, tare da gayyatar masu neman mukamai su shiga ƙungiyar.
Ya ce duk wanda ke son zama gwamna, sanata, ɗan majalisar wakilai ko kansila zai iya shiga Rainbow Coalition domin samun damar siyasa.
Wike ya gargadi duk masu yunƙurin tayar da zaune tsaye a Rivers, yana cewa mutanen jihar za su kare muradunsu kuma ba za su yarda a ƙwace musu haƙƙoƙinsu ba.
Haka kuma ya yi kira ga ƴan siyasar da ke fushi da su dawo gida domin yin sulhu, yana mai cewa akwai damar haɗin kai domin cigaban Rivers, cewar Punch.
Wike ya magantu kan dan takara a Rivers
Mun ba ku labarin cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi karin haske game da batun fitar da dan takara ko goyon bayansa a jihar Rivers.
Wike ya ce bai goyi bayan kowa domin takarar gwamnan Rivers ta 2027 ba, yana jiran hadakar PDP da APC ta yanke matsaya.
Ya bayyana cewa ba su aiki tare da Gwamna Siminalayi Fubara, har yana zarginsa da karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi.
Asali: Legit.ng

