"Ina Tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo Ya Dura a kan Gwamnatin Abba

"Ina Tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo Ya Dura a kan Gwamnatin Abba

  • Ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi kakkausar suka kan yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a jihar
  • Ya ce hare-haren da ake kai wa al’umma a wasu ƙananan hukumomi sun nuna cewa rayuka da dukiyoyin jama’a ba sa samun kariya yadda ya kamata
  • Kwamred Aminu Gwarzo ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da suka addabi wasu yankunan Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NDC kuma tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalolin tsaro ke ƙara kamari a wasu sassan jihar.

Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana cewa a yanzu, bata garin mutane suna cin karensu babu babbaka wajen kai hare-hare a cikin birni da kauyukan jihar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 game da Aminu Gwarzo, wanda zai yi wa NDC takarar Gwamnan Kano

Gwarzo ya caccaki gwamnatin Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da tsohon mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Gwarzo ya ce abin takaici ne yadda hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen mutane suka zama ruwan dare a wasu yankuna, lamarin da ya ce ya jefa al’umma cikin fargaba.

Tsohon mataimakin gwamna ya soki Gwamnatin Kano

Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi zargin cewa gwamnati mai ci ba ta ɗauki matakan da suka dace wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba, duk da irin ƙorafe-ƙorafen da ake ci gaba da yi daga sassa daban-daban na jihar.

A cewarsa, wasu ƙananan hukumomi sun fuskanci hare-hare masu muni inda aka rasa rayuka tare da asarar dukiyoyi masu yawa.

A kalamansa:

“Abin da ke faruwa a wasu yankunan Kano abin damuwa ne ƙwarai. Akwai wuraren da aka kashe mutane da dama, aka kwashe dukiyoyinsu, wasu kuma aka yi garkuwa da su har yanzu ba a san makomarsu ba.”

'Dan takarar NDC ya shawarci gwamnatin jihar Kano

Kara karanta wannan

'Dan uwan Fubara ya fito neman takarar gwamnan Ribas, ya yi wa jama'a alkawari

Kwamred Gwarzo ya kuma yi ikirarin cewa matsalolin tsaro ba su tsaya a yankunan karkara kaɗai ba, domin a cewarsa har cikin birnin Kano ana samun rahotannin kashe-kashe da hare-hare lokaci zuwa lokaci.

Ya ce hakan na nuna cewa akwai buƙatar sake nazari kan dabarun tsaron da ake amfani da su domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce:

“Mutane suna rasa rayukansu a wurare daban-daban, iyalai suna zaman makoki, al’umma kuma suna rayuwa cikin tsoro. Wannan ya kamata ya zama abin da zai fi daukar hankalin gwamnati a yanzu."

Tsohon mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar, gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro na da muhimmanci wajen magance matsalolin da ke addabar jama’a.

Kano: Hanga ya yi magana kan rasa takara

A baya, mun kawo labarin cewa Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga, ya yi magana bayan an ba Nasiru Yusuf Gawuna tikitin takarar kujerar da ya ke kai domin ya tsaya a 2027.

Sanata Hanga ya ce an yi masa adalci kuma an cimma matsaya kan zaɓin Gawuna bayan tattaunawa domin Kwankwasiyya ta ci gaba tare da duba masalahar Nasiru Yusuf Gawuna da ya bar APC.

Ya jaddada biyayyarsa ga jagoran Kwankwasiyya, tare da bayyana cewa soyayyasa ga akidar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya ce idan akwai abin da ya fi takara, zai iya bayarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng