ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Ceto Daliban Borno Kamar na Oyo
- Jam'iyyar ADC ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da irin dabarar da aka ceto dalibai da malamai a Oriire wajen kubutar da sauran mutanen da aka sace
- Jam'iyyar ta ce bai kamata nasarar da aka samu a jihar Oyo ta kasance ta musamman ba, sai dai ta zama ma'aunin yadda gwamnati za ta magance dukkan sace-sacen mutane
- ADC ta bayyana cewa iyalai a jihohin Kwara, Borno, Zamfara, Kaduna, Neja da Benue na ci gaba da jiran kubutar da 'yan uwansu da ke hannun masu garkuwa da mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jam'iyyar ADC ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fadada dabarar tsaro da ta kai ga ceto dalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo zuwa sauran sassan Najeriya.
Jam'iyyar ta ce ya kamata irin wannan tsari ya zama ma'aunin yadda gwamnatin tarayya za ta magance dukkan al'amuran garkuwa da mutane a fadin kasar nan.

Source: Facebook
The Cable ta rahoto cewa ADC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Juma'a.
Batun ceto daliban Oyo
Sanarwar ta biyo bayan kalaman da Shugaba Tinubu ya yi lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya daga jihar Oyo karkashin jagorancin Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A yayin taron, shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ki tattaunawa da masu garkuwa da mutanen, inda ta dogara da ayyukan jami'an tsaro domin ceto wadanda aka sace.
Bolaji Abdullahi ya ce jam'iyyar ta yi maraba da nasarar da aka samu, amma ta tambayi dalilin da ya sa ba a amfani da irin wannan dabara wajen kubutar da sauran mutanen da aka sace a wasu jihohi.
Ya ce:
"Kowane dan Najeriya ya kamata ya yi farin ciki da wannan nasarar da gwamnatin tarayya ta samu. Ceto kowace rayuwa daga hannun masu garkuwa da mutane nasara ce ga kasa baki daya."
Kiran da ADC ta yi ga Tinubu
Abdullahi ya ce har yanzu daruruwan iyalai a jihohin Kwara, Borno, Zamfara, Kaduna, Neja da Benue na cikin damuwa saboda 'yan uwansu da ke hannun masu garkuwa da mutane.
Tribune ta rahoto ya ce wadannan iyalai ba sa neman wata kulawa ta musamman, sai dai a dauke su daidai da sauran 'yan kasa.
A cewarsa, shugaban kasa ya kamata ya nuna irin kudurin da ya nuna a aikin ceton mutanen Oriire a duk sauran al'amuran garkuwa da mutane.

Source: Twitter
Ya ce:
"Ceton mutanen Oriire bai kamata ya zama wani labari na musamman da gwamnati za ta rika alfahari da shi ba. Ya kamata ya zama ma'aunin yadda ake mayar da martani ga sace mutane a Najeriya."
Soyinka ya yi korafi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Farfesa Wole Soyinka, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin sake bude fayel din binciken kashe-kashen da ba a warware ba.
Soyinka ya ce ci gaba da gaza hukunta masu aikata irin wadannan laifuffuka na karfafa rashin hukunci tare da rage amincewar jama'a da tsarin shari'a.
Ya kuma bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba domin tabbatar da an yi adalci ga dukkan wadanda aka kashe ba bisa ka'ida ba.
Asali: Legit.ng


