Adamawa: Sarkin Mota Ya Samu Takara a NDC, Za a Fafata da Shi a Zaben 2027
- Aliyu Mohammad, wanda aka fi sani da Sarkin Mota ya bayyana cewa sun amsa kiran jama'a na fito wa takara domin a wakilce su a zaben 2027
- Matashin 'dan siyasar ya lashe zaɓen fitar da gwani na kujerar wakilan tarayya a mazabar Yola North/Yola South/Girei karkashin jam'iyyar NDC
- Ya bayyana cewa nasarar da aka samu ta dukkanin magoya bayansa ne a karkashin Sarkified tare da alkawari ga 'yan mazabarsa idan suka zabe shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Adamawa - Aliyu Mohammad, wanda aka fi sani da Sarkin Mota, ya samu nasarar lashe zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar NDC.
Wannan na nufin Sarkin mota zai yi takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Yola ta Arewa, YolataKudu da Girei a jihar Adamawa.

Source: Facebook
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X bayan ayyana sakamakon zaɓen, Aliyu Mohammad ya ce yana matuƙar godiya ga al'ummar mazabar da suka nuna masa amincewa tare da ba shi damar wakiltar jam'iyyar a zaɓen 2027.
Sarkin Mota ya samu takara a NDC
A cikin sakonsa, Sarkin Mota ya ce nasarar da ya samu ta nuna cewa al'umma sun yi magana tare da bayyana ra'ayinsu kan makomar siyasar yankin.
Ya ce:
"Alhamdulillah. Al'umma sun yi magana, kuma na yi matuƙar godiya da amincewar da suka nuna mani."
Hon. Aliyu Mohammad ya kuma miƙa godiyarsa ga dukkannin magoya baya, abokai da masu ruwa da tsaki da suka tsaya tsayin daka wajen ganin tafiyar da ya fara ta cimma nasara.
Ya ce wannan nasara ba ta mutum ɗaya ba ce, illa nasara ce ta kowa da kowa da ya yi imani da manufar sauyi da ci gaban da yake son kawowa.
Alkawarin Sarkin Mota ga mutanensa
Da yake bayyana abin zai sakaa gaba, Aliyu Mohammad ya ce al'ummar Yola ta Arewa Yola ta Kudu da Girei za su shaida irin wakilcin da ya dace da muradunsu idan suka ba shi dama a babban zaɓe mai zuwa.
Ya jaddada cewa burinsa shi ne tabbatar da an ji muryar jama'a tare da samar da ci gaba da zai amfani yankin baki ɗaya.

Source: Facebook
Sarkin Mota ya ce:
"Wannan nasara tamu ce baki ɗaya. Na gode wa duk wanda ya yi imani da wannan tafiya kuma ya tsaya tare da mu."
Ya ƙara da cewa:
"Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei za su ga yadda ingantaccen wakilci yake. Wannan shi ne farkon tafiya."
Sarkin Mota ya kuma bayyana cewa tafiyar da ake kira 'Sarkified Movement' na ci gaba da samun karɓuwa, yana mai cewa nasarar da aka samu alama ce ta sabon babi a siyasar yankin.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnoni 7 da suka samu tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC a zaben 2027
Ya sake gode wa magoya bayansa bisa jajircewarsu da goyon bayan da suka ba shi tun daga farkon fafutukar neman tikitin jam'iyyar.
NDC ta ba Marafa takara
A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar NDC ta ayyana Sanata Kabiru Marafa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Zamfara a babban zaben 2027 da ake shirin gudanar wa nan da watanni masu zuwa.
Tsohon sanatan Zamfara ta Tsakiya ya samu tikitin NDC ne ta hanyar tsarin masalaha, inda shugabanni da magoya baya suka amince da shi, inda shi kuma ya gode wa shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar NDC.
Shugabannin jam’iyyar NDC da magoya baya sun hallara domin shaida yadda aka amince da shi a matsayin ɗan takarar gwamna a zaben 2027, tare da fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu idan lokaci ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

