Bayan Kotu Ta Share wa Jonathan Hanya, PDP Ta Buɗe Masa Ƙofar Komawa Aso Villa
- Tsagin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ta sanya rana domin tabbatar da takarar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan
- Wannan na zuwa ne bayan Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da ke kalubalantar cancantar Jonathan tsayawa takara a zaɓen 2027
- Rikicin cikin gida ya ƙara tsananta a PDP yayin da ɓangaren da Nyesom Wike ke marawa baya ya ayyana Sandy Onor a matsayin ɗan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ta bayyana cewa za ta tabbatar da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a babban zaɓen 2027.
Wannan na kunshe a cikin sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ɓangaren Turaki a PDP, Ini Ememobong, tare da sakataren tsare-tsare na jam’iyyar, Theophilus Shan suka fitar a ranar Alhamis,28 ga watan Mayu, 2026.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce za a gudanar da taron musamman na ƙasa a Abuja ranar Asabar, 30 ga watan Mayu, 2026 domin tabbatar da Jonathan a matsayin ɗan takara.
Tsagin PDP zai tabbatar da takarar Jonathan
PM News ta kawo labarin cewa jam’iyyar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan amincewar da aka bai wa Jonathan kasancewarsa shi kaɗai ne ya nemi tikitin shugaban ƙasa a ƙarƙashin ɓangaren Turaki na PDP.
Tun a ranar 19 ga watan Mayu, 2026 ne jam’iyyar ta sanar da cire sharadin tantance Jonathan kafin ba shi damar tsayawa takara.
PDP ta ce kasancewar Jonathan tsohon shugaban ƙasa ne, babu buƙatar sake tantance shi kafin shiga takara.

Source: Twitter
A ranar Talata 26 ga watan Mayu, 2026 kuma, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi fatali da ƙarar da aka shigar domin hana Jonathan tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Mai shari’a Peter Lifu wanda ya jagoranci shari’ar ya ce wanda ya shigar da ƙarar, JohnMary Jideobi, bai da hurumin doka na kai ƙarar saboda bai nuna wata asara kai tsaye da ya yi sakamakon shirin Jonathan na tsayawa takara ba.
Rikici ya raba jam'iyyar PDP
Bangaren Turaki na PDP ya yaba wa hukuncin kotun, yana mai cewa hukuncin ya yi daidai da doka da kuma hankali.
Jam’iyyar ta ce dokoki ba sa aiki kan abubuwan da suka gabata, tana mai cewa hukuncin ya share wa Jonathan hanya domin ci gaba da abin da ta kira “aikin ceto Najeriya”.
Jonathan ya taba shugabancin Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015 kafin ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari a zaɓen 2015.
Sai dai rikicin cikin gida ya ci gaba da dabaibaye PDP, inda jam’iyyar ta kasu gida biyu, domin tuni ɓangaren Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya fitar da dan takara.
Tsagin ya sanar da marawa tsohon Sanata Sandy Onor baya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ɓangaren lamarin ya nuna yadda rikicin shugabanci da rabuwar kai ke ƙara ƙamari a PDP.
Sule Lamido ya gargadi Jonathan
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi fatali da kiraye-kirayen da ake yi wa Goodluck Jonathan kan ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.
Sule Lamido, wanda jigo ne a PDP da ake ganin Jonathan zai iya neman takara a cikinta ya ce kiran ya samo asali ne daga takaicin halin da siyasar Najeriya ke ciki a halin yanzu.
Tsohon gwamnan ya gargadi Jonathan da kada ya bari yabon mutane ko neman faranta masa rai ya sa ya koma siyasar jam’iyya yanzu domin za a fi bukatar jagorancinsa a nan gaba
Asali: Legit.ng


