Nnaji: Ministan da Tinubu Ya Kora saboda Jabun Takardu Ya Samu Takarar Gwamna a PDP
- Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji ya samu nasara a zaben fitar da 'dan takarar gwanna na jam'iyyar PDP a jihar Enugu
- Tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya tabbatar da Nnaji a matsayin dan takarar gwamnan a karkashin inuwar PDP a zaben 2027
- 'Dan siyasar dai ya rasa kujerarsa ta minista ne sakamakon zargin da ake masa na amfani da takardun digiri da na NYSC na bogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu, Nigeria - Tsohon Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Enugu na jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2027.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta tsaida Nnaji takarar gwamnan Enugu duk da zargin amfani da jabun takardun karatu ciki har da takardar digiri da ke kansa.

Source: UGC
Tsohon ministan Tinubu ya samu tikitin PDP
Sai dai takararsa ta fito ne daga ɓangaren PDP mai biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito ta kawo.
Nnaji ya samu ƙuri’u 7,424 inda ya kayar da wani mai neman takara, Samson Nnamani, wanda ya samu ƙuri’u 600 a zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a Enugu ranar Litinin.
Shugabar kwamitin zaɓen na PDP a jihar, Austin Nwachukwu, ce ta jagoranci sanar da sakamakon a birnin Enugu.
Dalilin zargin Nnaji da jabun takardu
A watan Oktoban 2025, Premium Times ta wallafa wani bincike da ya zargi Nnaji da amfani da jabun takardun digiri da na NYSC, waɗanda ya miƙa wa Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Dattawa yayin tantance shi a matsayin minista.
Rahotanni sun nuna cewa ya sauka daga muƙaminsa kwanaki uku bayan fitowar binciken.
Daga baya ya koma PDP daga APC, jam’iyyar da ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashinta a zaben 2023 amma bai yi nasara ba.
Rahotanni sun kuma ce kwamitin bincike da Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya kafa ya gano cewa Nnaji ya yi amfani da jabun takardun digiri da na NYSC.
Abin da ya faɗa bayan samun tikitin PDP
Da yake jawabi bayan nasararsa, Nnaji ya yi alƙawarin rage wahalhalun al’ummar Enugu idan aka zaɓe shi gwamna a 2027.
“Na sadaukar da wannan nasara ga Ubangiji da mutanen Enugu waɗanda aka danne cikin shekaru uku da suka gabata tare da ɗora musu haraji masu yawa,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya ce masu gidaje, masu otel da masu baburan haya suna kuka saboda haraji, yana mai cewa gwamnati ya kamata ta tallafa wa marasa galihu maimakon ƙara musu nauyi.
Nnaji ya sake jaddada cewa idan ya zama gwamna zai yi wa’adi guda na shekara huɗu kacal.
PDP ta tsaida dan takarar gwamnan Kano
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta kammala zaben fitar da dan takarar gwamna a jihar Kano, kuma ta sanar da sakamako a ranar Litinin.
Mohammed Sani Abacha, babban ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya sha kaye a ƙoƙarinsa na samun tikitin takarar gwamnan Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Abacha ya sha kaye ne a hannun Muhammad Bello Dalhatu bayan gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar adawa ta PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

