Ta Faru Ya Ƙare: Gwamna Bala Ya Bar PDP, Ya Faɗi dalilin Shiga Sabuwar Jam'iyyarsa

Ta Faru Ya Ƙare: Gwamna Bala Ya Bar PDP, Ya Faɗi dalilin Shiga Sabuwar Jam'iyyarsa

  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan hukuncin Kotun Koli
  • Gwamnan ya tabbatar da komawa jam'iyyar APM tare da magoya bayansa bayan taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati
  • Kafin sauya shekar zuwa APM, Bala Mohammed shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, lamarin da ya jawo hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da sauya shekar sa daga jam’iyyar PDP zuwa Allied Peoples Movement, wato APM.

Majiyoyi suka ce gwamnan ya fice ne tare da magoya bayansa masu biyayya ga bangaren Tanimu Turaki kwanaki biyu bayan hukuncin Kotun Koli kan rikicin shugabanci.

Gwamna Bala ya watsar da jam'iyyar PDP
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi yayin taro a gidan gwamnati. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a gidan gwamnatin Bauchi yayin da shugaban jam’iyyar na kasa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Kwankwaso ya gama yanke shawara, zai bar ADC tare da Peter Obi

Gwamna Bala ya magantu bayan hukuncin kotu

Hakan ya biyo bayan sanarwar Sanata Bala Mohammed, cewa zai fita daga jam'iyyar adawa ta PDP sakamakon hukuncin Kotun Daukaka Kara.

Ya bayyana cewa zai koma zuwa wata jam’iyya ta dabam nan ba da jimawa ba, domin a cewarsa lokaci na neman kurewa 'yan adawa.

Bala Mohammed ya kuma sanar da kujerar da zai nema a zaben 2027 a lokacin da aka yi masa tambaya a kan ko zai nemi shugaban kasa.

Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ba zai yi takarar shugaban kasa ba a 2027, domin a PDP ma sun mayar da batun tsayawa takara zuwa Kudu.

Gwamna Bala Mohammed ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APM
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi yana jawabi yayin taro. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Shugaban APM ya karbi Gwamna Bala

Shugaban jam'iyyar APM na kasa, Yusuf Dantalle, ya tsaya tare da shi gaban jama’a inda ya tarbe shi da yi masa maraba da zuwa cikinta domin ba da ta gudunmawa.

Sanarwar sauya shekar ta biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a boye tsakanin shugabannin siyasa da manyan jiga-jigan jam’iyyar a Bauchi, cewar Punch.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamnan Bauchi zai sauya sheka, ya fida kujerar da zai nema a 2027

Kafin ficewarsa daga PDP, Bala Mohammed yana rike da mukamin shugaban kungiyar gwamnonin PDP, wanda ke daya daga cikin manyan mukamai a jam’iyyar adawa.

Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan Mohammed daga bangaren shugabancin Tanimu Turaki su ma sun bi sahunsa zuwa jam’iyyar APM a jihar Bauchi.

Sauya shekar gwamnan ya jawo ce-ce-ku-ce a siyasar Najeriya, musamman ganin matsayin da Bala Mohammed yake da shi a cikin PDP kafin wannan mataki.

Gwamna Bala ya raba motoci ga sarakuna

A wani labarin, an ji cewa Gwamnan Bauchi, Bala Mohammaed ya raba motoci ga sarakunan gargajiya a lokacin da alkaluman NBS ke cewa akwai bakin talauci a jihar.

Rahoton hukumar kididdiga ta kasa ta NBS ya nuna cewa sama da 70% na jama’a na rayuwa cikin talauci ta fuskoki da dama, da suka hada da samun abin kashewa.

Yara da mata sun fi fuskantar matsaloli, musamman a bangaren ilimi da lafiya, wanda hakan ya sa kyautar motocin ta sake daukar hankulan jama'a duba da ganin halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.