Babbar Sallah: Gwamna Buni Ya Yi Wa Musulmi Nasiha, Ya Tabo Rayuwar Annabi Muhammad SAW
- Gwamna Mai Bala Buni ya bukaci al'ummar Musulmi su yi koyi da halayen fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW)
- Mai Bala Buni ya kuma roki jama'a da su dage da addu'ar Allah Ya kawo zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a jihar Yobe da Najeriya baki daya
- Gwamnan ya yi wannan nasiha ne a sakonsa na barka da Sallah jim kadan bayan sallar idi a birnin Damaturu jiya Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yobe, Nigeria - Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya haɗu da ɗaruruwan Musulmi yayin da ya halarci filin idi domin yin babbar Sallah (Eid-el-Kabir) a Damaturu, babban birnin jihar.
Babban Limamin Masallacin Yobe, Malam Hudu Muhammad Yusuf, ne ya jagoranci sallar Idi raka’a biyu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada ranar Laraba.

Source: Facebook
Nasihar da Gwanma Mala Buni ya yi
A rahoton Leadership, Buni ya ce manufar sallar layya ita ce tunawa da koyi da sadaukarwa, biyayya da miƙa wuya ga Allah da Annabi Ibrahim (AS) ya nuna lokacin da ya amince ya sadaukar da ɗansa Isma’il (AS).
Ta bakin wakilinsa kuma mataimakin gwamnan Yobe, Idi Barde Gubana, Gwamna Buni ya ce cikin rahamar Allah ne aka samar da rago domin maye gurbin Annabi Isma’il (AS) a wancan lokacin.
Ya yi kira ga musulmi da su yi koyi da halayen Annabawa musamman Annabi Muhammad (SAW).
Mala Buni ya roki a dage da addu'a
Gwamna Buni ya yi kira ga jama’a da su ƙara yawaita addu’o’i domin samun zaman lafiya, ci gaba da bunƙasar jihar Yobe da ƙasa baki ɗaya, musamman a wannan lokacin na bukukuwan Sallah.
Haka kuma ya buƙaci al’umma su ci gaba da yi wa Yobe da Najeriya addu’ar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziƙi.
Liman ya ja hankali kan zumunci
A hudubar da ya gabatar bayan sallar Idi, Sheikh Hudu Muhammad Yusuf ya tunatar da jama’a cewa babbar Sallah rana ce mai girma a kalandar Musulunci.
Ya ƙarfafa Musulmi da su riƙa kai ziyara ga iyalai, abokai, maƙwabta da ‘yan uwa a lokacin bukukuwa, yana mai cewa hakan na ƙarfafa zumunci da haɗin kai a cikin al’umma.

Source: Facebook
Shehin malamin ya kuma yi addu’ar Allah Ya tabbatar zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen 2027 a ƙasar nan, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Daga ƙarshe, ya buƙaci iyaye da masu kula da yara su sanya ido sosai kan ‘ya’yansu a lokacin bukukuwan domin hana su shiga faɗa da sauran miyagun halaye.
APC ta tsaida magajin Gwamna Buni
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ayyana tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe, Baba Malam Wali a matsayin dan takarar gwamna a zaben 2027.
An ayyana Malam Wali mai shekaru 68 a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamna da aka gudanar a fadin kananan hukumomin Yobe.
Malam Wali ya samu ƙuri’u 236,711 inda ya doke sauran masu neman takarar ciki har da Dr. Abubakar Bukar Kagu wanda ya samu ƙuri’u 9,748.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


