‘Asali Layya na Kiristoci ne’: Fasto Ya Jawo Magana game da Babbar Salla

‘Asali Layya na Kiristoci ne’: Fasto Ya Jawo Magana game da Babbar Salla

  • Fitaccen faston CAC a Najeriya ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana wasu sababbin bayanai game da sallar layya
  • Faston ya ce Annabi Ishaqa da Isma’il ‘ya’yan Annabi Ibrahim ne da suka fi kusanci da Kiristoci, yana danganta hadayar Ishaqa da addinin Kirista
  • An bayyana muhimmancin watan Zul-Hijja da bikin Ojude Oba a Ijebu-Ode, yayin da Musulmai ke shirin gudanar da bikin babbar salla

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Wani faston cocin CAC a Najeriya ya jawo maganganu yayin da ya yi wasu kalamai da suka shafi addinin Kiristanci da sallar layya.

Faston ya bayyana cewa bikin layya wanda da Yarbawa ke kira Ileya ya fi dangantaka da addinin Kiristanci.

Fasto ya ce ainihi layya ta Kiristoci ce ba Musulmi ba
Babban rago da aka tanada za a yanka saboda sallar layya. Hoto: Contributor.
Source: Getty Images

Fasto ya jawo maganganu kan maganar layya

Malamin cocin ya bayyana a wani bidiyo da ya karade TikTok cewa Annabi Ishaqa da Isma’ilu, ‘ya’yan Annabi Ibrahim, sun fi kusanci da Kiristoci fiye da Musulmai.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Ya ce labarin hadayar Ishaqa ne tushen fahimtar Kiristanci game da sadaukarwa, ya bukaci Kiristoci kada su guji cin naman Sallah idan makwabta suka ba su.

Faston ya kara da cewa zuwan Annabi Isa Almasihu da sadaukar da kansa a kan gicciye ne ya kawo karshen irin wannan hadaya a Kiristanci.

Ya ce jinin Almasihu ya wanke zunuban mabiya addinin Kirista tare da jiran dawowarsa domin ya cece su daga wannan duniyada ake ciki mai tarin zunubai.

Musulmi za su yi bikin babbar salla gobe Laraba
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Facebook

Musulmai za su fara layya daga ranar Laraba

Rahotanni sun bayyana cewa Musulmai za su gudanar da bikin babbar salla na shekarar 2026 ranar Laraba 27 ga watan Mayu.

Wannan biki na yanka a sallar layya yana tuna hadayar da Annabi Ibrahim ya yi saboda biyayya ga Allah.

An kuma bayyana muhimmancin watan Zul-Hijja a addinin Musulunci, inda ake gudanar da ibadu a Makka da Madina musamman ga wadanda suka samu damar zuwa kasa mai tsarki.

Wadanda ba su samu damar zuwa Hajji ba kan yi layya a kasashensu tare da yanka domin samun ladar layya daga wurin Allah.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Tinubu ya cancanci 'yan Najeriya su kara ba shi dama a zaben 2027

Yadda ake bikin Ojude a yankin Yarbawa

Har ila yau, al'ummar Yarabawa na bikin Ojude Oba wanda ake gudanarwa a Ijebu-Ode bayan sallah wanda ke samun halartar mutane da dama daga yankin Yarbawa.

Dubban mutane daga sassa daban-daban na duniya kan halarci bikin al’adun Yarbawa mai kayatarwa wanda ke daukar hankalin al'umma sosai da ke yankin Kudu maso Yamma.

Darusa 10 na ranar Arfa ga Musulmi

Mun kawo muku rahoton cewa a ranar Talata, 9 ga watan Zul Hijja watau 26 ga watan Mayun 2026 miliyoyin al'ummar Musulmi da suka samu zuwa aikin Hajji za su gabatar da hawan Arafa a Makkah.

Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu muhimman darusa da Musulmi za su koya a ranar.

Malamin ya ambaci darusan dukufa neman gafarar Allah, yi wa juna afuwa da wasu abubuwa da ya kamata kowane Musulmi ya yi a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.