"Ko Ganduje ba zai Ce Shi ba Yarona ba ne": Kwankwaso Ya Yi Martani ga Abba
- Rikicin siyasa tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da ɗaukar sabon salo a jihar Kano
- Kwankwaso ya yi martani ga kalaman Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya ke ganin kamar raini ne a kira shi da 'yaro'
- A bayanin da ya yi, gwamna Abba Yusuf ya gargadi Kwankwaso da ya mutunta kansa, yana mai cewa shirunsa ba alamar tsoro ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya kuma jigo a jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake mayar da martani ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kan takaddamar da ke tsakaninsu ta siyasa.
Kwankwaso ya bayyana cewa babu wani abin mamaki idan ya kira wasu mutane “yaransa” a siyasa, domin a cewarsa ya taimaka wajen ɗaga su zuwa manyan muƙamai.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan na Kano ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road a Kano ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026 kamar yadda hadiminsa, Hon Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook.
Kwankwaso ya ce Abba yaronsa ne
Da yake magana ga magoya bayansa, Kwankwaso ya ce wasu mutane suna nuna rashin ladabi idan suka ƙi amincewa cewa sun taɓa zama yaransa a siyasa.

Source: Twitter
Ya ce:
“Na ji wasu suna cewa ba sa son a kira su yara. Idan ba rashin kunya ba, ta yaya Mai Gidan Ruwa ko Aminu Goro za su ce ba yarana ba ne a siyasa?"
Kwankwaso ya ƙara da cewa Ganduje, wanda ya yi wa’adin shekaru takwas a matsayin mataimakinsa kafin daga baya ya zama gwamna, yana cikin mutanen da suka amfana da tafiyarsa ta siyasa.
"Ta yaya ma Ganduje zai musanta cewa ya taɓa zama yarona?”

Kara karanta wannan
Tsohon hadimin shugaban APC na kasa, Mustapha Dawaki ya bi tafiyar Kwankwaso a Kano
Dangantaka na tsami tsakanin Abba da Kwankwaso
Kalaman Kwankwaso na zuwa ne bayan Abba Gida Gida ya yi shi ne karo na farko da ya fito fili yana sukar Kwankwaso tun bayan rabuwar da aka samu tsakaninsu a farkon wannan shekarar.
Gwamnan ya ce yawan kalaman da Kwankwaso ke yi a kansa sun yi yawa, amma shirun da ya yi bai kamata a ɗauke shi a matsayin tsoro ba.
Haka kuma ya gargadi jagoran Kwankwasiyyar da ya mutunta kansa, in ba haka ba zai fito ya bayyana wasu abubuwa da ke ɓoye. Tun bayan da Gwamna Yusuf ya rabu da Kwankwaso, tsohon ubangidansa na siyasa ya riƙa zarginsa da cin amanar tafiyar Kwankwasiyya.
Kwankwaso ya ce Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar lashe zaɓe ne a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, amma daga baya ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Takaddamar da ke tsakanin jagororin biyu na ci gaba da jan hankalin al’ummar Kano, yayin da masu bibiyar siyasa ke sa ido kan yadda rikicin zai kaya gabanin zaɓukan 2027.
Tsohon mataimakin gwamna ya magantu kan Abba
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi magana kan sabanin da ya shiga tsakaninsa da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Tsohon mataimakin gwamnan ya soki manufar “Kano First” tare da cewa tsaro ya kara tabarbarewa a jihar Kano, inda ya bayyana cewa an dauko tsarin 'yan mulkin mallaka ne a jihar Kano.
Kwamred Aminu Abdulsalam, wanda ya yi murabus daga mukaminsa ya bayyana matsayarsa game da neman kujerar tsohon mai gidansa a jam'iyyar NDC yayin da ake fitar da 'yan takara.
Asali: Legit.ng

