Mutane Sun Soki Mai Neman Takara a NDC kan Kona ‘Bible’ da Sukar Kiristanci

Mutane Sun Soki Mai Neman Takara a NDC kan Kona ‘Bible’ da Sukar Kiristanci

  • Wasu matasa da shugabannin yankin Uzo Uwani a jihar Enugu sun nuna damuwa kan halayyar wani mai neman takara a NDC
  • Yan yankin sun yi watsi da kudirin Matthias Ezeaku na takarar majalisar wakilai saboda kalamansa kan addinin Kirista har ma da Musulunci
  • Kungiyar Concerned Uzo-Uwani Youths ta ce kona Littafi Mai Tsarki da suka danganta da Ezeaku na iya haddasa rikicin addini da rabuwar kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uwani, Enugu - Wasu matasa da shugabanni daga karamar hukumar Uzo Uwani a jihar Enugu sun caccaki wani mai neman takara a NDC.

Matasan sun yi watsi da Matthias Ezeaku, mai neman tikitin NDC na majalisar wakilai a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Mai neman takara a NDC ya sha suka kan caccakar Kiristanci
Mai neman takara a NDC, Matthias Ezeaku da jagororin jam'iyyar. Hoto: Matthias Ezeaku, Obi Kwankwaso.
Source: Facebook

Rahoton Premium Times ya ce mutanen sun ce furucinsa na kin addinin Kirista da kona Littafi Mai Tsarki abin damuwa ne ga zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

An kashe mutum 8 bayan dan majalisa ya bada kyautar miliyoyin Naira a jihar Neja

Korafin kungiya kan neman takarar Matthias Ezeaku

Kungiyar 'Concerned Uzo-Uwani Youths' ta bayyana cewa Ezeaku ya dade yana sukar Kiristanci da Musulunci tare da yada addinin gargajiya.

Sun gargadi cewa irin wadannan kalamai masu tayar da hankali za su iya haddasa rikicin addini da rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma.

Sai dai Ezeaku ya bayyana adawar da ake yi masa a matsayin farfaganda, yana mai kare matakinsa na kona Littafi Mai Tsarki.

Ya ce kamar yadda wasu Kiristoci ke kona kayan tsafi da gumaka, haka kowa ke da damar kin abin da ya daina bi a addini.

Shugaban kungiyar, Chukwuma Obinna, ya ce matasan sun nuna damuwa kan abin da suka kira “ci gaba da yada karya kan addini da kalaman kiyayya ga Kiristoci da Musulmai.

Kungiyar ta zargi Mista Ezeaku da yawan yin kalamai masu tunzura jama’a kan addinin Kirista da sauran akidu na addini.

Sun gargadi cewa irin wannan hali na iya zama babbar barazana ga zaman lafiya da hadin kai a mazabar, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

ADC ta fitar da sanarwa, Atiku na shirin fafatawa da masu neman takarar 2027

A cewarsu, sukar shugabannin Kirista da suka kan koyarwa da ayyukan addinin Kirista, ciki har da kona Littafi Mai Tsarki, abin damuwa ne sosai.

Wani masoyin Obi ya gamu da matsala kan neman takaea
Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi yayin kamfe. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Yadda dan siyasar ke sukar Musulunci, Kiristanci

Mai neman takarar kujerar majalisar wakilai na jam’iyyar NDC ya shafe shekaru yana sukar addinin Kirista a fili.

Ya kasance yana tallata bautar gargajiya tare da bayyana Kiristanci da Musulunci a matsayin addinan yaudara da baki da aka kawo domin batar da ‘yan Afirka.

Shi dai dan asalin garin Nrobo ne da ke karamar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu, watajiha da ke Kudu maso Gabashin Najeriya mai yawan mabiya addinin Kirista.

An gano wanda Kwankwaso ke son ba takara

Mun ba ku labarin cewa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin bayyana sunan wanda zai yi takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Kano.

Da farko an yi tsammanin tsohon 'dan takarar gwamna, Nasiru Gawuna ne zai samu kujerar, sai dai an yi masa tayin mataimakin gwamna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Gawuna ya ƙi tayin kujerar mataimakin gwamna da ta Sanatan Kano ta Tsakiya kuma ya fadi matsayarsa a NDC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.