Amaechi Ya Yi Watsi Da 'Shiryayyen' Zaben Fitar da Gwanin ADC da Atiku Ya Ci

Amaechi Ya Yi Watsi Da 'Shiryayyen' Zaben Fitar da Gwanin ADC da Atiku Ya Ci

  • Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC, yana zargin an hana yawancin mambobi kada kuri’a a jihohi daban-daban
  • Ya ce sakamakon da ake sanarwa “an kirkire shi”, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta bambanta da APC ba idan aka tafka magudi
  • Mohammed Hayatu-Deen ma ya ki halartar sanar da sakamakon zaben, yana zargin an yi magudi da rubuta sakamakon karya a wasu yankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi ya yi magana kan zabe fitar da gwani.

Amaechi ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka gudanar ranar Litinin 26 ga watan Mayun 2026.

Amaechi, Hayatu-Deen sun soki zaben fitar da gwanin ADC
Yan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi, Mohammed Hayatu-Deen da Atiku Abubakar. Hoto: ADC Vanguard.
Source: Twitter

A wata sanarwa da ya fitar wanda TheCable ta samu, Amaechi ya zargi cewa an hana mutane da dama kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Zaben ADC: Atiku Abubakar ya shiga gaba, ya samu gagarumar nasara a jihohi 5

Amarchi ya tabbatar da cewa an tafka magudin zabe a yankuna daban-daban da ke fadin Najeriya.

Jam’iyyar ADC ta gudanar da zaben kai tsaye domin zakulo dan takarar shugaban kasa na 2027, inda Atiku Abubakar, Mohammed Hayatu-Deen da Amaechi suka fafata sosai.

Ya bayyana cewa sakamakon da ake sanarwa “an kirkire shi”, yana mai cewa ba zai amince da tsarin da bai kasance gaskiya da adalci ba.

Amaechi ya ce tun farko ya bayyana cewa zai amince da sakamakon ne kawai idan an gudanar da zaben cikin gaskiya, adalci da kuma cikakken bayyana gaskiya.

Ya ce babu yadda za a yi a hana kusan kaso tamanin cikin dari na mambobin jam’iyya kada kuri’a sannan a sa ran zai amince da irin wannan sakamako.

Dan takarar ya ce manufar ADC ita ce bai wa talakawa damar bayyana ra’ayoyinsu tare da ceto Najeriya daga rashin shugabanci da zalunci.

Amaechi ya ce jam’iyyar da ke sukar APC da INEC kan magudi da sayen kuri’u ba za ta iya aikata irin wadannan abubuwa ba.

Kara karanta wannan

Zaben fitar da gwani: Atiku ya samu gagarumar nasara kan Amaechi a Gombe

A halin yanzu, jami’an tattara sakamakon zaben fidda gwani na ADC sun fara isa cibiyar tattara sakamako da ke otal din Transcorp Hilton.

Rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar ne ke kan gaba bayan samun nasara a jihohi fiye da goma ciki har da Gombe, Abia, Sokoto da Zamfara.

Tun da farko, Mohammed Hayatu-Deen ya sanar cewa ba zai halarci sanar da sakamakon zaben ba saboda abin da ya kira magudi da rashin gaskiya.

Ƙarin bayani na tafe ...

Atiku ya lashe zabe a Gombe

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi a ADC a Gombe.

Jami’in tattara sakamako, Farfesa David Agbu, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana yayin da mutane 140,949 suka kada kuri’unsu.

Rotimi Amaechi ya samu kuri’u 1,150, yayin da Muhammad Hayatu-Deen ya samu 465 a zaben da jami’an INEC suka sanya ido a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.