Zaben Fitar da Gwani: Atiku Ya Samu Gagarumar Nasara kan Amaechi a Gombe

Zaben Fitar da Gwani: Atiku Ya Samu Gagarumar Nasara kan Amaechi a Gombe

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi a ADC a Gombe
  • Jami’in tattara sakamako, Farfesa David Agbu, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana yayin da mutane 140,949 suka kada kuri’unsu
  • Rotimi Amaechi ya samu kuri’u 1,150, yayin da Muhammad Hayatu-Deen ya samu 465 a zaben da jami’an INEC suka sanya ido a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An fara samun sakamakon zaben fitar da gwani na ADC a matakin shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi nasara a Gombe yayin zaɓen fitar da gwani.

Atiku ya lashe zaben fitar da gwani a Gombe
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a taron ADC. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Atiku Abubakar ya yi nasara a Gombe

Atiku ya lashe zaben ne na shugaban kasa a jam’iyyar ADC da aka gudanar a dukkan kananan hukumomi 11 na Gombe, ya samu kuri’u 139,334, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Zaben ADC: Atiku Abubakar ya shiga gaba, ya samu gagarumar nasara a jihohi 5

Jami’in tattara skamakon zaben na jihar, Farfesa David Agbu, ya bayyana sakamakon a yammacin Litinin.

Farfesan ya ce Atiku ya doke Rotimi Amaechi da Muhammad Hayatu-Deen a fafatawar da aka gudanar cikin lumana.

A cewar Farfesa Agbu, Amaechi ya samu kuri’u 1,150 yayin da Muhammad Hayatu-Deen ya samu kuri’u 465.

Ya kara da cewa mambobi 140,949 ne suka kada kuri’a daga cikin 160,982 inda ya cewa Atiku ne ya fi kowa yawan kuri’u saboda haka aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa na ADC da aka gudanar ranar 25 ga Mayu, 2026, cewar Punch.

Tun farko jam’iyyar ADC a Gombe ta bayyana Atiku a matsayin dan takara guda daya kafin gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa a fadin jihar baki daya.

Amaechi ya sha kaye a zaben fitar da gwani a Gombe
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Rotimi Amaechi. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Source: Twitter

Godiya da jam'iyyar ADC ta yi ga al'umma

Jami’in tattara sakamakon ya gode wa mambobin jam’iyyar ADC saboda hakurin da suka nuna yayin tattara sakamako.

Ya ce kofar daukaka kara a bude take ga duk dan takarar da bai gamsu ba domin neman adalci kafin babban zaben da za a gudanar a 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya lallasa yan takara 2, ya samu nasara a zaben fitar da gwanin ADC a Sakkwato

An bayyana sakamakon ne a gaban jami’an hukumar INEC, jami’an tsaro da shugabannin jam’iyya daban-daban da suka halarci taron sanar da sakamakon zaben a Gombe.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai tsohon ministan sufuri, Sanata Idris Abdullahi Umar, wanda shi ne dan takarar sanata na ADC a Gombe ta Tsakiya tare da sauran shugabannin jam’iyyar.

Atiku ya yi nasara a jihar Sokoto

A baya, mun ba ku labarin cewa an fara samun sakamakon zaben fitar da gwanin jam'iyyar ADC na takarar shugaban kasa a jiya Litinin 25 ga watan Mayun 2026.

Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u 68,823 inda ya kayar da sauran ‘yan takarar da suka fafata, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen a Sokoto.

Daga cikin manyan kusoshin da suka halarci wurin tattara sakamakon akwai tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.