Pantami Ya Fice daga Jam'iyyar APC, Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna a Jihar Gombe

Pantami Ya Fice daga Jam'iyyar APC, Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna a Jihar Gombe

  • Farfesa Isa Ali Pantami ya sauya sheka daga APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Gombe bayan rasa rikitin takara
  • Tsohon ministan na sadarwa ya kuma samu tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a zaben 2027 karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP
  • Masu ruwa da tsakin PDP a Gombe ne suka tabbatar da Pantami a matsayin dan takarar gwamna a wani taro da aka gudanar yau Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar Gombe.

Bayan sauya shekarsa, Pantami ya kuma ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2027 da ke tafe.

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami a taron da PDP ta tsaida shi takara a jihar Gombe Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

PDP ta tsaida Pantami takarar gwamna

Kara karanta wannan

Nnaji: Ministan da Tinubu ya kora saboda jabun takardu ya samu takarar gwamna a PDP

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an ayyana Sheikh Pantami a matsayin dan takarar gwamnan PDP ne ta hanyara amincewa da baki a zaben fitar da gwanin da aka gudanar ranar Talata a Gombe.

Mambobin jam'iyyar PDP ne suka amince da bai wa tsohon ministan takara ba tare fa hamayya ba a yau Talata, 26 ga watan Mayu, 2026.

Shugaban kwamitin zaɓe na Jam'iyyar PDP, Hon. Gregory Yenlong, ya ayyana shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe, bayan da ya kasance ɗan takara guda ɗaya tilo da ya nemi takara

Pantami ya daukar wa mutanen Gombe alkawari

Da yake jawabi jim kaɗan bayan bayyana shi a matsayin 'dan takara, Pantami ya bayyana cewa ya fito neman kujerar gwamna ne domin ya bayar da tashi gudunmawar wajen yi wa al'ummar jihar hidima.

Ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi a 2027, zai gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A yanzu Pantami zai fafata da Jamilu Gwamna, ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC da sauran masu neman mulki a jihar Gombe

Tun farko dai Pantami ya soki tsarin da ya bai wa Gwamna tikitin takarar APC ta hanyar maslaha.

Kara karanta wannan

2027: Mohammed Abacha ya sha kaye, PDP ta tsaida dan takarar gwamna a jihar Kano

Pantami.
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami a wurin taron tabbatar masa da takara a APC Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Ya nemi a gudanar da zaɓen fitar da gwani kai tsaye, amma ya janye daga takarar kwana guda kafin zaɓen, yana zargin rashin gaskiya da adalci a tsarin.

Masu neman takara a PDP sun nuna adawa

Bayan kammala zaɓen fitar da gwani a APC, wasu ‘yan takarar gwamna huɗu na PDP sun nuna damuwa kan yunkurin shigar da Pantami cikin takarar gwamna ta PDP.

Sai dai duk da wannan adawa, shugabannin PDP a jihar Gombe sun zaɓi Pantami a matsayin wanda zai ɗaga tutar jam’iyyar a zaɓen gwamna na 2027.

ADC ta tsaida dan takara a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa wani dan kasuwa kuma dan siyasa, Dr Bala Bello Tinka, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar ADC a jihar Gombe.

Da yake jawabi jim kadan bayan ayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar, Bala Tinka ya nuna godiyarsa bisa amincewa da kuma yarda da mambobin jam’iyyar suka nuna masa.

Ya yi alkawarin samar da shugabanci nagari tare da aiwatar da ayyukan da suka shafi rayuwar talakawa kai tsaye idan ya yi nasara a zabe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262