2027: An Gano ana Kullawa Tinubu Makarkashiya a Jihohin Kudu

2027: An Gano ana Kullawa Tinubu Makarkashiya a Jihohin Kudu

  • 'Yan siyasa daga yankuna daban daban na Najeriya na cigaba da tattaunawa kan makomar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a babban zaben 2027
  • Jigo a jam'iyyar APC kuma abokin Bola Tinubu, Aremo Olusegun Osoba ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya da ake shirin kulla masu a Kudu
  • Aremo Olusegun Osoba da ya ke tsohon gwamnan jihar Ogun ne ya yi magana ne a lokacin da ake fadan sakamakon zaben fitar da gwani da APC ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Jigon APC kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Aremo Olusegun Osoba, ya yi zargin cewa ana kullawa shugaba Bola Tinubu makarkashiya a Kudancin Najeriya a zaben shugaban kasa na 2027.

Osoba ya ce makircin na da nufin fito da ‘yan takarar shugaban kasa daban-daban daga Kudancin kasar domin rage tasirin Tinubu.

Kara karanta wannan

'Ba za mu bar 'yan adawa ba,' Tinubu ya magantu kan zaben 2027

Daily Trust ta rahoto cewa Osoba ya bayyana haka ne a Abeokuta yayin sanar da sakamakon zaben fitar gwani na shugaban kasa da jam’iyyar APC ta yi a jihar Ogun.

Zaben APC a jihar Ogun

A zaben fitar da gwani da aka gudanar a kananan hukumomi 20 na jihar Ogun, shugaba Bola Tinubu ya samu kuri’u 322,485 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Stanley Osifo wanda bai samu ko kuri’a daya ba.

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da ya jagoranci aikin tattara sakamakon zaben ne ya sanar da sakamakon a gaban shugabannin APC da suka hada da Osoba a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Mataimakiyar gwamna, Noimot Salako-Oyedele, karamin ministan lafiya da walwalar jama’a Dr Iziak Salako da sauran shugabannin jam’iyyar sun halarci taron.

Zargin yi wa Tinubu makarkashiya

Kafin sanar da sakamakon, Osoba ya bukaci ‘ya’yan APC da su shirya domin abin da ya kira “ainihin zabe” da zai zo a watan Janairu mai zuwa.

Osoba ya ce akwai kuskuren fahimta tsakanin wasu ‘ya’yan APC cewa Tinubu ba shi da abokin hamayya a zaben da ke tafe. Ya gargadi shugabannin jam’iyyar da kada su yi sakaci saboda makiya suna da yawa.

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

Ya yi zargin cewa takarar Peter Obi, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wani bangare ne na yunkurin raba kuri’un Kudancin Najeriya domin rage karfin Tinubu.

A cewarsa:

“Ina son rokonmu gaba daya yayin da muke tunkarar zabe mai zuwa da kada mu yi sakaci. Mutane da dama suna cewa ba mu da abokin hamayya, amma wannan fahimta ce mara kyau. Makiyan suna da yawa.
Lokacin da aka sanar da sakamakon zaben fitar da gwani na APC a Ogun
Gwamna Dapo Abiodun yana sanar da sakamakon zaben fitar da gwani na APC a Ogun. Hoto: Prince Dr. Dapo Abiodun - MFR
Source: Facebook

Maganar Tinubu kan zaben 2027

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gargadi 'yan Najeriya da kar su zabi 'yan jam'iyyar adawa a 2027.

Shugaba Tinubu ya ce ya kammala dauko hanyar gyara Najeriya wajen kawo cigaba a fannoni da dama a shekarun da ya shafe a kan mulki.

Saboda haka ya yi gargadi da cewa idan aka zabi 'yan adawa za su mayar da hannun agogo baya ta hanyar gaza cigaba da daura kasar a kan turba mai kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng