"Za Su Yi Amfani"; Shugaban INEC Ya Ba Masu Kada Kuri'a Tabbaci kan Zabe a Najeriya
- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi tsokaci kan zaben shekarar badi
- Farfesa Amupitan ya bayyana cewa kuri'un masu zaben za su yi amfani wajen dangwalo 'dan takarar da suke so
- Shugaban na hukumar INEC ya yi jawabai ne yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke Kudancin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ekiti - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Josh Amupitan, ya yi magana kan gudanar da zabe.
Farfesa Joash Amupitan ya tabbatar wa mutanen da suka cacanci yin zaɓe cewa ƙuri’unsu za su yi amfani.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci kwamishinonin kasa na hukumar INECa wata ziyarar auna shirin tunkarar zaɓe a jihar Ekiti gabannin zaɓen gwamna na ranar 20 ga watan Junin 2026.

Kara karanta wannan
"Ban nemi zama mataimakin Atiku ba": An fusata Rotimi Ameachi da tambayar tikitin ADC
Joash Amupitan ya mika rajistar masu zabe
A wurin taron, shugaban na hukumar INEC ya mika rajistar masu zaɓe a hukumance ga jam’iyyun siyasa, jaridar Leadership ta kawo rahoton.
Farfesa Joash Amupitan ya siffanta taron a matsayin “na musamman kuma mai matuƙar muhimmanci” ga hukumar INEC.
Amupitan ya bayyana cewa wata dama ce da ba a cika samu ba a ce jihar Ekiti ta karbi bakuncin Shugaban INEC tare da kusan dukkan kwamishinonin kasa domin wallafawa da kuma miƙa rajistar masu zaɓen.
“Dokar zaɓe ta tanadi cewa kwanaki 30 kafin zaɓe, dole ne a wallafa rajistar masu zaɓe kuma a miƙa ta ga jam’iyyun siyasa."
- Farfesa Joash Amupitan
Amupitan ya magantu kan zaben Ekiti
Shugaban na INEC ya bayyana cewa, daga cikin manyan ayyuka guda tara da ke ƙunshe cikin jadawalin zaɓe da aka fitar a shekarar da ta gabata, an riga an kammala guda bakwai cikin nasara, yayin da yaƙin neman zaɓe zai ƙare a hukumance ranar 18 ga watan Junin 2026.

Kara karanta wannan
Shugaban majalisar dattawa ya yi wa 'yan Arewa barazana kan zaben 2027? Gaskiya ta fito
Amupitan ya siffanta rajistar masu zaɓen a matsayin “harsashin da ake gina zaɓuka masu ’yanci, adalci, da sahihanci a kai,” yana mai jaddada cewa ingancinta da mutuncinta suna da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da cewa an ji muryar kowane mai zaɓe da ya cancanta.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa an tattara rajistar masu zaɓen ne bayan tsauraran matakai na tattara bayanai, cikakkiyar tantancewa, da kuma ayyukan tace bayanai cikin tsanaki.
Jam'iyyun siyasa sun cika sharadin INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa jam'iyyun siyasa 22 sun cika sharuddan da ta gindaya.
A cewar INEC, jam'iyyun siyasa 22 a Najeriya sun cika sharadin da dokar zabe ta shimfida na mikawa mata sunayen mambobinsu.
INEC ta sanar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa 22 da aka yi wa rajista sun mika kundin rajistar mambobinsu domin bin tanadin dokar zabe ta 2026 gabanin babban zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng