Shugaban APC Ya Gana da Bola Tinubu yayin da Rigingimu Suka Dabaibaye Jam'iyyar
- Jam'iyyar APC ta bayyana yakinin cewa za ta warware duk wasu matsaloli da rikice-rikicen da suka biyo bayan zabukan fitar da yan takara
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas
- Ana ci gaba da samun sabani da rigingimun tsakanin masu neman takara a inuwar APC, inda wasu ke nuna fushinsu a fili kan tsarin masalaha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar na da hanyoyin da za ta bi wajen warware rikice-rikicen da suka biyo bayan zabukan fitar da gwani da ake gudanarwa a fadin kasar nan.
Farfesa Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai bayan wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Lagos ranar Laraba.

Source: Facebook
APC ta gode wa Tinubu da mambobinta
A rahoton Daily Trust, shugaban APC ya bayyana cewa zabukan fitar da gwani na bana su ne mafi gasa a tarihin Najeriya saboda yadda jam’iyyar ta samu karbuwa a sassan kasar nan.
Ya gode wa Shugaba Tinubu da magoya bayan jam’iyyar APC bisa goyon bayan da suka bayar, yana mai cewa an gudanar da zabukan cikin tsari da kwanciyar hankali.
Yilwatda ya ce:
“Ina kuma gode wa magoya bayanmu saboda yadda suka nuna da’a wajen gudanar da wannan tsari. An samu karancin rikici sosai, kuma an gudanar da komai cikin tsari.
APC ta yi magana kan tsarin maslaha
Dangane da ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan tsarin maslaha a wasu jihohi, Yilwatda ya ce dokokin jam’iyyar sun fayyace yadda ake tafiyar da tsarin, cewar rahoton Vanguard.
“Dokokinmu game da tsarin maslaha a bayyane suke, haka nan dokokin zabe kato bayan kato ma a bayyane suke. Idan maslaha ba ta yiwu ba, sai a koma a yi zabe, kuma hakan ake yi a jihohi,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu na amfani da kudin da ya ci bashi wajen gina ababen more rayuwa a Najeriya
APC ta shirya shawo kan masu korafi
Yilwatda ya amince cewa za a samu wasu ‘yan jam’iyya da ba za su gamsu da sakamakon zabukan ba, amma ya ce APC na da kwamitocin sulhu da za su sasanta rikice-rikice bayan zabukan fitar da gwani.
“Tabbas za a samu wasu da za su ji haushi bayan wadannan zabuka. Muna da tsarin warware rikice-rikice na cikin gida wanda ya dade yana aiki.
“Muna da Kwamitin Sulhu na Shugaban Kasa da kuma Kwamitin Sulhu na Jam’iyya. APC na aiki tukuru domin rage rikice-rikice da kula da bukatun jama’a gwargwadon iko,” in ji shi.

Source: Twitter
Sanatan APC ya yi fatali da zaben fitar da gwani
A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Eteng Williams ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen fitar da gwani na APC a Cross River ta Tsakiya.
Ya ce babu wani zaɓe da aka gudanar a ko ɗaya daga cikin mazaɓu 66 na yankin Cross River ta Tsakiya, yana mai cewa duk wani sakamako da ake yaɗawa ba shi da tushe.
Eteng Williams ya buƙaci shugabannin APC na ƙasa su binciki yadda aka gudanar da tsarin domin kare mutuncin jam’iyyar gabanin 2027
Asali: Legit.ng
