Akwa Ibom
Gwamnatin Akwa Ibom ta sallami Osborne Okon, mai taimaka wa mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa, bayan ya ce ya kamata Bola Tinubu ya yi murabus.
Tsohon minista, John James Udoedehe ya ce talauci da rashin aikin yi ne suka sa yake neman takarar gwamnan Akwa Ibom a karkashin jam’iyyar ADC a 2027.
Hukumar INEC ta sauya wa dan uwan Nyesom Wike, Anugbum Onuoha wurin aiki zuwa Akwa Ibom a matsayin sabon kwamishinan zabe, bayan ya karɓi ragamar aiki.
Gwamnan Akwai Ibom, Pastor Umo Eno, ya yi barazanar kwace takardun sarautar sarakunanan gargajiya idan suka bari aka samu barnata kayan gwamnati a jihar.
Kotun jihar Enugu ta yankewa wani fasto hukuncin kisa kan laifin kashe wani dalibin jami'a. Alkalin kotun ya ce abin takaici ne malamin addini ya kashe rai.
Tsohon mai ba jam'iyyar PDP shawara kan harkokin shari'a na kasa, Emmanuel Enoidem, ya sasanta rikicinsa da Godswill Akpabio. Ya sauya sheka zuwa APC.
Tsohon sanata kuma jagora a jam'iyyar ADC ta jihar Akwa Ibom, Sanata Akpanudoedehe ya bukaci Gwamna Umo Eno ya yi murabus kan rikicin dajin Ekid.
Tashin hankali ya barke a yankin Ekid da ke Akwa Ibom, bayan kama Princess God’sown Udoito, mai sukar Gwamna Umo Eno kan batun filaye da muhalli.
Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tana duba kudirin dokar da zai haramta zina a tsakanin mutane.
Akwa Ibom
Samu kari