"Ba Ruwan Yan Sandan Jihohi da Zaben 2027": Gwamnatin Kano

"Ba Ruwan Yan Sandan Jihohi da Zaben 2027": Gwamnatin Kano

  • Gwamnatin Kano ta ce 'yan sandan jihohi ba za su kasance da alaka da zabukan 2027 ba kamar yadda wasu ke fargaba ba bayan umarnin shugaban kasa
  • Hadimin Gwamna a kan kafafen yada labarai, Ahmed S Aruwa ya tabbatar wa Legit cewa akwai dalilan da suka sa dole aka kirkiri yan sandan jihohi
  • Ya bayyana cewa jami'an rundunar jihohi ba za su shafe na tarayya da ake da ita ba, saboda haka zai yi wahala a gansu kan akwatunan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa babu abin da zai hada 'yan sandan jihohi da za a kafa da rumfunan zaben 2027.

Kalaman sun zo ne bayan gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nanata cewa jiharsa a shirye take domin tabbatar da samar da 'yan sandan jihohi ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

Gwamnatin Kano ta raba yan sandan jihohi da aikin zabe
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito yadda Gwamnan ya ce Kano ta shirya, kuma tana da kayan aiki da kuma isassun ma'aikatan da za su iya aiki a rundunar 'yan sandan jihohi.

An shirya wa 'yan sandan jihohi a Kano

Hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Ahmed S. Aruwa, ne ya tabbatar wa Legit hakan a wata hira da ya yi tare da wasu kafafen yada labarai a jihar Kano, inda ya ce babu dalilin da zai sa a ji tsoron kafa 'yan sandan jihohi.

A cewarsa:

"Sai ka tambaya me ya sa aka yi? Na farko, an yi ne saboda rashin tsaro. Kuma ana ganin cewa duk lokacin da ka samu 'yan sanda a jiharka, su ne suka fi sanin lungu da sako da dukkan yankunan jihar."
"Yanzu idan ka dauki dan sanda a jihar Kano, mutumin Gwale ya san Gwale, mutumin Municipal kuma ya san Municipal."
Gwamnati ta ce za a yi aiki yadda ya dace wajen magance rashin tsaro
Hadimin gwamnan Kano kan kafafen yada labarai Ahmed S Aruwa Hoto: Ahmed S Aruwa
Source: Facebook

Ahmed S. Aruwa ya bayyana cewa samar da 'yan sandan jihohi zai taimaka wajen tura jami'ai zuwa lungu da sako da kuma dazuka da suka saba da su, domin tabbatar da ingantaccen tsaro.

Kara karanta wannan

'Kwankwasiyya ce ta daga Abba': NDC na shirin fattakar gwamnatin Kano a 2027

Ba ruwan 'yan sanda da zabe – Gwamnatin Kano

A hirar, hadimin gwamnan Kano ya kara da cewa babu alaka tsakanin 'yan sandan jihohi da zabukan 2027 ko wani zabe da za a gudanar a Najeriya.

Ya ce akwai rashin fahimta kan batun, domin ana gudanar da zabe ne duk bayan shekara hudu, yayin da babban aikin rundunar shi ne tabbatar da tsaro.

Ahmed S. Aruwa ya kara da cewa tun da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ce ke gudanar da zabe, 'yan sandan gwamnatin tarayya ne za su kula da tsaron zabuka, ba 'yan sandan jihohi ba.

Gwamnatin Kano ta yi babban aiki

A baya, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da hedikwatar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) da ake sa ran za ta bayar da gagarumin taimako ga ci gaban lafiya.

Abba Gida Gida ya kuma bude sabuwar cibiyar kula da masu cutar sikila ta Abba Care, wadda ita ce irinta ta farko a Arewacin Najeriya da za ta rika bayar da kulawa ta musamman ga masu dauke da cutar.

Gwamnatin jihar ta fara rabon na’urorin zamani 3,000 na auna hawan jini ga manyan ma’aikata da masu rike da mukaman siyasa yayin da ta ce tana kokarin kara kyautata alaka da mutanen da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng