Talauci da rashin aikin yi shine yake kara haddasa shaye - shaye a kasar nan
Talauci da rashin aikin yi ga matasa sune manyan dalilan da suke kawo shan miyagun kwayoyi da kayan maye a kasar nan, kamar yanda hukumar lafiya ta yankin Afrika ta yamma ta bayyana
Talauci da rashin aikin yi ga matasa sune manyan dalilan da suke kawo shan miyagun kwayoyi da kayan maye a kasar nan, kamar yanda hukumar lafiya ta yankin Afrika ta yamma ta bayyana, a wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai, don tunawa da ranar kwayoyi ta duniya, hukumar ta nuna damuwarta na shaye shaye da kuma safarar kwayoyi a Najeriya.
DUBA WANNAN: Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff
Tayi kira da a dauki matakin gaggawa gurin samar da daidaitaccen yanayin samar da kwayoyin da zasu amfani lafiya, tsaro da kuma zaman lafiyar yan Najeriya.
Hukumar ta jinjiinawa kokarin da gwamnatin tarayya, ma'aikatar lafiy , hukumar NAFDAC da kuma NDLEA suke gurin yaki da kalubalen da ake fuskanta na shan miyagun kwayoyi da kuma safarar su a Najeriya.
Ta jinjiinawa ofishin shugaban majalisar dattawa akan dokoki biyu da suka mika akan lafiyar kwakwalwa da shaye shaye.
Hukumar tayi kira ga gwamnati da tayi watsi da duk wasu dokokin da suke goyon bayan shan miyagun kwayoyi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng