"Kada a Zalunci El Rufa'i": Tsohon Jigon APC Ya Roki Dattawan Arewa Su Saka Baki
- Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar APC, Timi Frank ya bukaci a bi doka da adalci wajen tsare tsohon gwamna Nasir El-Rufai
- Timi Frank ya bayyana cewa dole ne a bai wa tsohon gwamnan damar shirya kare kansa ba tare da muzguna wa ko tauye masa hakki ba
- Ya roki dattawan Arewa da kungiyoyi su nemi a sako Malam El-Rufai wanda hukumomin Najeriya suka tsare shi saboda zarge-zarge da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa
Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Timi Frank, ya bukaci hukumomi su tabbatar da bin ka’ida da adalci wajen tafiyar da lamarin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ke hannun hukumar DSS.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2026, Frank ya ce ya dace a kare hakkokin El-Rufai tare da ba shi isasshen lokaci domin shirya kare kansa.

Kara karanta wannan
"Ana rasa abinci a gidana": Ministan Buhari, Amaechi ya magantu kan mulki a Najeriya

Source: Facebook
A ruwayar jaridar Punch, Timi Frank ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya mika kansa ga hukumomin tsaro da kansa bayan dawowarsa Najeriya daga kasar Masar.
Tsohon kakakin APC ya magantu kan Nasir El-Rufa'i
A cewar Timi Frank, yaki da cin hanci da rashawa abu ne mai kyau, amma dole ne a gudanar da shi bisa tsarin doka da oda.
Ya ce:
“Ba wannan ne karo na farko da nake bayyana goyon bayana ga yaki da cin hanci da rashawa ba. Amma adalci, gaskiya, bin doka da kuma bin ka’ida bai kamata a yi watsi da su a kowanne hali ba.”
Tsohon jigon APC din ya kara da cewa jami’an tsaro su gudanar da binciken cikin kwarewa da kuma gaskiya, yana mai cewa duk wani mataki da za a dauka kan El-Rufai ya kamata ya kasance karkashin adalci da rikon amana.
El-Rufa'i: Timi Frank ya roki manyan Arewa
Kwamred Timi Frank ya kuma yi kira ga dattawan Arewa, matasa, kungiyoyin fararen hula da kuma kasashen duniya su sa baki domin ganin an sako El-Rufai.
Ya ce:
“Ina addu’ar dattawan Arewa da matasa ba za su zauna suna kallon wani abu mara kyau ya faru da Malam El-Rufai ba.”

Source: Twitter
Haka kuma ya roki kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan su sanya ido kan yadda ake tafiyar da batun tsare tsohon gwamnan.
Frank ya bayyana El-Rufai a matsayin fitaccen dan siyasa wanda ya taka muhimmiyar rawa a zaben shekarar 2023, yana mai bukatar ‘yan Najeriya su ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa dangane da tsare shi.
DSS ta kara kama Nasir El-Rufa'i
A baya kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya fada hannun jami'an hukumar tsaro ta fararen kaya, wato DSS bayan kammala zaman babbar kotun tarayya a Abuja.
Hakan dai na zuwa ne biyo bayan belin da aka ba tsohon gwamnan a zaman kotu na ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 bayan lauyoyinsa sun dade suna rokon a bayar da belinsa.
Hajiya Aisha Nasir El-Rufai, daya daga cikin matan tsohon gwamnan ta bayyana irin barazanar da suke fuskanta tun bayan kama mijinsu, ta kuma roki DSS ta bi umarnin kotu ta sake shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
