"Ana Rasa Abinci a Gidana": Ministan Buhari, Amaechi Ya Magantu kan Mulki a Najeriya

"Ana Rasa Abinci a Gidana": Ministan Buhari, Amaechi Ya Magantu kan Mulki a Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi ya soki kalaman shugaban kasa kan batun “yaƙi” da ‘yan siyasa gabanin zaben 2027
  • Amaechi, wanda ya rike kujerar minista a zamanin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai lokutan da yake komawa gida babu abin da za a ci
  • Tsohon ministan sufurin Rotimi Amaechi, ya nuna damuwa kan wasu kalaman shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai dace a rika tsorata jama'a ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi ya dura a kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana kansa a matsayin hatsabibin 'dan siyasa.

Amaechi ya bayyana cewa baidace shugaban kasa ya rika amfani da furucin da zai iya jefa tsoro a zukatan jama’a ko 'yan adawa da ke tsarin dimokuradiyya ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Rotimi Amaechi ya ce yana iya rasa abinci
Rotimi Amaechi, mai neman tikitin takarar shugaban kasa a ADC Hoto: Rotimi Amaechi
Source: Facebook

Amaechi ya yi wannan bayani ne a hira da ya yi da Tashar Trust TV, inda ya ce shugaban kasa ya kamata ya zama abin kwanciyar hankali ga dukkannin ‘yan kasa maimakon amfani da kalaman da za su tayar da hankula.

Amaechi ya magantu kan kalaman Tinubu

Instablog ta wallafa bidiyo inda Rotimi Amaechi ya bayyana takaici tare da zargin cewa Bola Ahmed Tinubu yana yi wa jama'a barazana.

A cewarsa:

“Ta yaya shugaban kasa zai gaya wa ‘yan kasarsa cewa zai yi yaƙi da su? Idan shugaban kasa ya zauna ya ce zan ayyana yaƙi, zan kashe dukkan ku ‘yan siyasa, to ba ya sake zama shugaban kasa saboda ba mu da tsaro a hannunsa.”

Sai dai an tuna masa cewa Tinubu ya taba bayyana kansa a matsayin “ɗan siyasa mai taurin kai,” amma Amaechi ya ce bai dauki hakan a matsayin wata barazana ba.

Kara karanta wannan

"Ka guji tarko": Sule Lamido ya shawarci Jonathan game da takarar shugaban kasa

Amaechi ya soki yan Najeriya
Tsohon minista, Rotimi Amaechi, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Rotimi Amaechi/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya ce:

“Mu ‘yan siyasa masu tawali’u ne.”

'Ina jin yunwa' - Amaechi

A wani bangare da ya dauki hankulan mutane, Amaechi ya bayyana cewa yana fuskantar matsin rayuwa irin na sauran ‘yan Najeriya, yana mai cewa akwai kwanakin da yake komawa gida ba tare da abin da zai ci ba.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana nufin “yunwar mulki” ne, sai ya ce:

“A’a, yunwar abinci nake nufi.”

Ya kara da cewa:

“Dana yana nan. Akwai kwanakin da nake dawowa gida ba ni da abin da zan ci.”

Amaechi ya kuma yi magana kan burinsa na shugabanci, inda ya jaddada cewa neman mulki bai kamata ya zama sanadin tashin hankali ko zubar da jini ba.

Ya ce ya dauki darasi daga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, wanda ya taba bayyana cewa neman shugabanci bai kamata ya haddasa rasa rayukan jama’a ba.

Amaechi ya magantu kan takara a 2027

Kara karanta wannan

"Ban nemi zama mataimakin Atiku ba": An fusata Rotimi Ameachi da tambayar tikitin ADC

A baya, mun wallafa cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce bai sayi fom domin ya zama mataimakin shugaban kasa ba a zaben 2027 a inuwar jam'iyyar ADC ba.

Amaechi ya nuna rashin jin dadinsa kan rade-radin cewa zai iya zama abokin takarar Atiku Abubakar a jam’iyyar ADC yayin da jam'iyyar ke shirin tunkarar zabe mai zuwa da sauran yan adawa.

Yana wannan batu ne bayan shi kansa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar sun sayi fom domin fafata wa a neman tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC gabanin 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng