Bayan Turmusa Ta a Zaɓen Osun, APC Ta Faɗi Matakin da Za Ta Ɗauka Nan Gaba

Bayan Turmusa Ta a Zaɓen Osun, APC Ta Faɗi Matakin da Za Ta Ɗauka Nan Gaba

  • APC ta Osun ta ce tana nazarin sakamakon zaɓen gwamna na 2026 daga mazabu 332, domin duba yiwuwar kai ƙara kotun zaɓe
  • Jam’iyyar ta ce tana tuntubar lauyoyinta kafin yanke shawarar mataki na gaba, tana mai cewa dokar ƙasa ta ba waɗanda suka ƙorafi damar neman adalci
  • APC ta bukaci magoya bayanta su kwantar da hankula, sannan ta roƙi ’yan sanda su kare mambobinta da magoya bayanta daga duk wata fitina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Jam’iyyar APC reshen Osun ta ce tana nazarin sakamakon zaɓen gwamna na 2026 a faɗin mazabu 332 na jihar.

Ta ce tana duba hanyoyin da doka ta tanada, ciki har da yiwuwar ƙalubalantar sakamakon zaɓen a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

APC tana duba yiwuwar zuwa kotu
Mambobin jam'iyyar APC da ɗan takarar gwamnan Osun. Hoto: Bola Oyebamiji.
Source: Twitter

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jam’iyyar, Cif Kola Olabisi, ya sanya wa hannu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso ya ce kan INEC bayan taya Adeleke murnar tazarce a Osun

Tuntubar da APC ke yi kan zaɓen Osun

APC ta ce tana tuntubar tawagar lauyoyinta kafin yanke shawarar matakin da za ta ɗauka bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana sakamakon zaɓen.

A cewar APC, tsarin zaɓe bai ƙare da sanar da sakamakon ba, domin tsarin kundin tsarin mulki ya bai wa waɗanda suka ƙorafi damar neman mafita.

Jam’iyyar ta ce waɗanda ba su gamsu ba na iya neman hakkinsu a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe, Kotun Ɗaukaka Ƙara, har ma da Kotun Ƙoli.

APC ta ce:

“Ba za a ce an kammala zaɓe ba, matuƙar ba a binciki dukkan hanyoyin shari’a da kundin tsarin mulki ya amince da su ba."

Ta ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen gyara duk wani kuskure da aka samu yayin gudanar da zaɓen, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026 da aka yi wa gyara ta tanada.

Jam’iyyar APC ta ce ba za ta yi jinkirin amfani da “damar da Dokar Zaɓe ta yanzu ta bayar” ba, bayan ta tuntubi lauyoyinta tare da bin shawarwarinsu.

Kara karanta wannan

Raɗaɗin faɗuwa: Yadda ƴan APC suka yi wa ɗan jarida dukan tsiya a rumfar zaɓe

APC za ta iya kai korafi kotu kan zaben Osun
Taswirar jihar da aka gudanar da zaɓen gwamna. Hoto: Legit.
Source: Original

APC ta magantu kan sanarwar INEC

APC ta bayyana matakin a matsayin wani ɓangare na kyawun dimokuraɗiyya, tana mai cewa sanarwar INEC ba za ta sa ta yi watsi da bin doka ba.

Ta ce ba za ta yi watsi da ƙudurin tabbatar da adalci da gaskiya ba, duk da cewa INEC ta bayyana sakamakon zaɓen gwamnan Osun.

Jam’iyyar ta yaba wa mambobinta da magoya bayanta saboda “juriya, basira da biyayya” da suka nuna a duk tsawon tsarin zaɓen.

Ta ce gudummawar da suka bayar ta taimaka wajen kai jam’iyyar wannan mataki a tarihin siyasar jihar, cewar Vanguard.

Sai dai APC ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankula, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Ta kuma bukace su da kada su mayar da martani ga duk wani abin da zai iya tayar da hankali daga mambobin jam’iyyar da ke mulki.

Kara karanta wannan

Ana kaɗa ƙuri'a a Osun, ƴan sanda sun faɗi tanadinsu kan zaben Bauchi

Yan APC sun ci zarafin ɗan jarida

An ji cewa wasu magoya bayan APC sun lakada wa ɗan jarida dukan yayin da yake aikin rahoto a zaɓen gwamnan jihar Osun.

Lamarin ya faru a rumfar zaɓen ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, inda aka kama Oluwafemi, aka mare shi tare da kwace katin shaidarsa.

’Yan sanda sun shiga tsakani domin kare ɗan jaridar, amma daga baya wani maharin sanye da kayan jami’in tsaro ya kore shi da bulala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.