Babbar Magana: INEC Ta Dauko Batun Takardun Karatun Shugaba Tinubu
- Hukumar INEC ta bayyana dalilin da ya sa ba a wallafa takardun firamare da sakandaren Shugaba Bola Tinubu cikin takardun da aka fitar ba
- Wani babban jami’in hukumar ya ce INEC kawao ta wallafa takardun da ’yan takarar suka gabatar mata
- Kalu Agu ya shigar da ƙorafi kan Tinubu, yana zargin ya gabatar da takardun shaidar karatu na bogi ga INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana dalilin da ya sa takardun shaidar makarantar firamare da sakandare na Shugaba Bola Tinubu ba su cikin takardun da aka wallafa na ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
Wani babban jami’in hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce INEC ta wallafa ne kawai takardun da ’yan takarar suka gabatar mata, kuma ba ta da ikon tambaya ko sauya takardun shaidar da aka miƙa mata.

Source: Twitter
Jami’in ya shaida wa jaridar The Punch cewa manufar wallafa takardun ita ce bai wa jama’a damar duba su tare da gabatar da ƙorafi idan suna da wata matsala da suka lura da ita.
“Abin da aka gabatar wa hukumar kawai muka wallafa. Ba mu da ikon tambayar waɗannan takardun. Abin da muka yi shi ne wallafa su domin duk wanda yake da ƙorafi ya iya bayyana matsalarsa kan abin da muka wallafa,” in ji jami’in
Abin da INEC ta ce
Wannan bayani na INEC ya biyo bayan tambayoyin da wasu ’yan Najeriya suka yi bayan hukumar ta wallafa takardun shaidar ’yan takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027.
An lura cewa takardun shaidar makarantar firamare da sakandare na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ba su cikin takardun da hukumar ta bayyana ga jama’a.
A cewar jami’in, INEC ba ta da hurumin yin tambayoyi ko sauya takardun da ɗan takara ya gabatar mata, sai dai ta wallafa su domin jama’a su duba tare da ɗaukar matakin da ya dace idan akwai abin da suke adawa da shi.
Kalu Agu ya shigar da korafi
Hakan na zuwa ne bayan, Kalu Agu, wani lauya kuma jigon ADC, ya shigar da ƙorafi kan Tinubu ga Hukumar Tarayyar Turai da ke Brussels, Belgium
Agu ya zargi Shugaban ƙasar da gabatar da takardun shaidar karatu na bogi ga INEC a matsayin wani ɓangare na sharuddan kundin tsarin mulki da ake buƙata domin takarar shugaban ƙasa a 2027
Sai dai bayanin da INEC ta yi ya nuna cewa takardun da hukumar ta wallafa sun dogara ne kan waɗanda ’yan takarar suka gabatar mata, yayin da duk wani ƙorafi kan bayanan da ke cikin takardun ko sahihancinsu za a iya gabatar da shi ta hanyoyin da doka ta tanada.

Source: Twitter
Adeleke ya yabawa Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bayan sake zabensa a matsayin gwamnan jihar a zaben da aka gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.
Gwamna Adeleke ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya kira shi domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben.
Asali: Legit.ng

