Baki Ya Yanka Wuya, Kotu Ta Ingiza Keyar Kakakin PDP zuwa Kurkuku kan Taba Gwamna
- Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Kwara ta tura sakataren yada labaran jam'iyyar PDP gidan yari kan zargin bata sunan gwamna
- Alkalin kotu ya ƙi bayar da belin Olusegun Olushola Adewara, saboda rashin bin ƙa’ida wajen gabatar da buƙatar bayan an aika shi gidan maza
- Sai dai jam'iyyar PDP ta fusata da wannan hukunci, inda a ke zargin gwamnatin Kwara da amfani da iko wajen murƙushe ‘yan adawan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kwara – Babbar kotun jihar Kwara da ke Ilorin ta bayar da umarnin tsare sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP a jihar, Olusegun Olushola Adewara.
An aika da Mista Olusegun Olushola Adewar zuwa gidan gyaran hali na Oke-Kura kan zargin bata sunan gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gurfanar da Adewara a gaban Mai shari’a T.S. Umar bisa tuhume-tuhume guda biyu.
Zargin da ake yi wa Kakakin PDP a Kwara
Jaridar Solacebase ta kawo labarin cewa ana zargin kakakin PDP da bata sunan gwamnan da kuma furucin da ake cewa ya haddasa hargitsi a tsakanin jama’a.
Masu gabatar da ƙara sun zargi kakakin jam’iyyar adawar da yin kalaman da gwamnatin jihar ta ɗauka a matsayin masu tayar da hankali da rashin jin daɗi.
Lauyan Adewara ya gabatar da buƙatar beli tare da yin bayanai a gaban kotu, amma Mai shari’a Umar ya ƙi amincewa da buƙatar, yana mai cewa ba a gabatar da ita yadda doka ta tanada ba.
Daga nan ne kotun ta bayar da umarnin a tsare shi tare da ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 10 ga watan Yunin 2026 domin sauraron buƙatar belin.

Kara karanta wannan
Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye
Kakakin PDP ya bayyana takaicinsa
Da yake magana bayan zaman kotun, Adewara ya bayyana takaicinsa kan matakin da aka ɗauka, amma ya ce zai mutunta tsarin shari’a duk da abin da ya kira alamar siyasa a shari’ar.

Source: Original
Adewara ya kuma roƙi magoya bayan PDP da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali.
Kakakin PDP, Adewara ya ce tsare shi ba zai raunana ƙudirin jam’iyyar adawa ba gabanin zaɓukan siyasa masu zuwa.
A cewarsa:
“Ina kira ga dukkannin magoya bayanmu da 'yan PDP a faɗin jihar su kasance masu bin doka da oda. Irin waɗannan lokuta wani ɓangare ne na sadaukarwar da ake buƙata wajen fafutukar kare dimokuraɗiyya da samar da kyakkyawar makoma ga Kwara kafin 2027.”
A cikin wata sanarwa da Mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Bashir Ashura, ya sanya wa hannu, PDP ta zargi gwamnatin jihar da amfani da ƙarfin gwamnati wajen gallaza masu sukar ta.
Jam'iyyar PDP ta samu koma baya
A baya, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gamu da koma baya bayan wasu daga cikin 'ya'yanta sun fice daga cikinta a jihar Oyo gabanin babban zaben 2027.
Wasu 'yan majalisar wakilai guda uku daga jihar sun sanar da murabus dinsu daga jam'iyyar wadda suka lashe zabe karkashinta a 2023, wanda hakan ya kara yawan adadin 'yan majalisar da suka bar PDP.
Tun da farko, wasu 'yan majalisa biyu na majalisar wakilai daga jihar Oyo, Anthony Adepoju, mai wakiltar mazaɓar Ibarapa ta Tsakiya/Arewa; da Ojo Makanjuola, mai wakiltar mazaɓar Ogo-Oluwa/Surulere, sun sanar da barin PDP.
Asali: Legit.ng

