PDP Ta Gamu da Koma Baya, 'Yan Majalisar Wakilai 3 Sun Fice daga Jam'iyyar

PDP Ta Gamu da Koma Baya, 'Yan Majalisar Wakilai 3 Sun Fice daga Jam'iyyar

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gamu da koma baya bayan wasu daga cikin mambobinta sun fice daga cikinta a jihar Oyo
  • Wasu 'yan majalisar wakilai guda uku daga jihar sun sanar da murabus dinsu daga jam'iyyar wadda suka lashe zabe karkashinta a 2023
  • Ficewarsu daga jam'iyyar ya kara yawan adadin 'yan majalisar wakilai da suka yi murabus daga PDP a cikin 'yan kwanakin nan

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Mambobin Majalisar wakilai guda uku daga jihar Oyo, sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar PDP mai adawa.

Najimdeen Oyedeji, mai wakiltar mazaɓar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa; Adedeji Olajide na mazaɓar Ibadan ta Arewa maso Yamma/Kudu maso Yamma; da kuma Abass Adigun na mazaɓar Ibadan ta Arewa maso Gabas/Kudu maso Gabas, sun yi murabus daga PDP.

Mambobin PDP sun ragu a majalisar wakilai
'Yan majalisa a yayin zama a majalisar wakilai Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa 'yan majalisar ba su sanar da jam'iyyar da za su koma ba.

Kara karanta wannan

Sanata a Kaduna ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar ADC

'Yan majalisar wakilai na PDP sun ragu

Tun da farko wasu mambobi biyu na majalisar wakilai daga jihar Oyo, Anthony Adepoju, mai wakiltar mazaɓar Ibarapa ta Tsakiya/Arewa; da Ojo Makanjuola, mai wakiltar mazaɓar Ogo-Oluwa/Surulere, sun sanar da murabus ɗinsu daga PDP.

Wannan sabon cigaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara raɗe-raɗin cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, na iya sauya sheƙa daga PDP zuwa jam’iyyar APM.

Sai dai, ’yan majalisar ba su bayyana jam’iyyar da za su koma ba, duk da rahotannin da ke alaƙanta yiwuwar komawarsu APM tare da gwamnan.

Meyasa suka fice daga PDP?

A cikin wasiƙarsa mai kwanan wata 5 ga watan Mayu wadda ya aika wa shugaban PDP na mazaɓa ta takwas ta Odinjo-Muslim, ƙaramar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas, Adigun ya bayyana "rikice-rikicen cikin gida masu dorewa waɗanda suka ci gaba da raunana jam’iyyar" a matsayin dalilinsa na ficewa.

Ɗan majalisar, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisa kan miyagun ƙwayoyi, ya ce lokacin da ya yi a PDP ya ba shi damar ƙulla dangantaka mai dorewa da kuma ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.

Kara karanta wannan

Bello El Rufai ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki, ya sake fitowa takara a zaben 2027

Olajide, a cikin ta sa wasiƙar murabus ɗin mai kwanan wata 5 ga watan Mayu zuwa ga shugaban PDP na mazaɓa ta 11 a ƙaramar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma, ya ce ya bar PDP ne bayan “tuntuɓa mai faɗi” da ya yi da abokan siyasa, magoya baya da mazaɓarsa.

Ana rade-radin Gwamna Seyi Makinde zai koma APM
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Sun yi shawara kafin barin PDP

Ya ƙara da cewa tun lokacin da ya shiga jam’iyyar, ya duƙufa "da dukkan zuciyarsa ga ci gabanta da nasarar zaɓe, wanda ya kai ga" samun nasararsa da "sake zaɓen sa" a karo na biyu a majalisar, jaridar Tribune ta kawo rahoton.

Hakazalika, Oyedeji a cikin ta sa wasiƙar zuwa ga shugaban PDP na mazaɓa ta biyar ta ƙaramar hukumar Kajola, ya ce ya yanke shawarar ne "cikin nuna damuwa" bayan "tuntuɓar da ta dace" daidai da ƙa’idodinsa da burinsa na siyasa.

Ɗan majalisar ya ce ya gode wa damammaki, abubuwan da ya koya da kuma dangantakar da ya samu lokacin da yake jam’iyyar.

Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa daya daga cikin sanatocin jihar Kaduna na PDP, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

Sanata Ibrahim Mustapha ya sanar da komawarsa jam'iyyar ADC bayan ya raba gari da PDP wadda ya lashe kujerar sanata a karkashinta.

Ya bayyana cewa rikicin shugabancin da ya addabi jam'iyyar na daga cikin dalilan da suka sanya ya fice daga cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng