Iran Ta Kawo Sabuwar Dabarar Ruguza Tsarin Kariyar Saman Amurka
- Gwamnatin kasar Iran ta inganta dabarun amfani da makamai masu linzami wajen kai hare-hare kan sansanonin Amurka a Gabas ta Tsakiya
- Rahotanni sun ce sababbin makamai masu linzamin Iran na iya sauya alkibla kwatsam, lamarin da ke ƙara wahalar da tsarin kariyar makamai na Amurka
- Hare-haren sun kuma tilasta wa Amurka amfani da makaman Patriot masu kare sansanoni cikin sauri, yayin da adadin waɗanda suka rage ke raguwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Iran ta inganta dabarun amfani da makamai masu linzami wajen kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke sassan Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun ce Iran na amfani da makamai masu linzami da za su iya sauya alkibla cikin gaggawa domin kauce wa tsarin kariyar makamai na Amurka.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Source: Getty Images
Iran ta sauya dabarun hare-hare
Roya News ta wallafa cewa hare-haren baya-bayan nan sun yi amfani da makamai masu linzami da ke iya sauya hanyar tafiyarsu a lokacin da suke gab da isa inda aka nufa.
Wannan dabarar ta matsa wa tsarin kariyar sansanonin Amurka lamba, tare da tilasta wa sojojin amfani da makaman Patriot masu kare sararin samaniya cikin sauri.
Rahotanni sun ce an riga an harba sama da makamai masu kare sararin samaniya na Patriot guda 1,500, yayin da ƙasa da 1,700 suka rage a hannun Pentagon.
Iran na ƙara ƙwarewa kan kai hari
Rahotanni sun bayyana Iran a matsayin abokiyar gaba da ke ƙara ƙwarewa wajen kauce wa tsarin kariyar Amurka.
Ana kuma zargin Iran da faɗaɗa hare-haren zuwa sassa daban-daban na Gabas ta Tsakiya tare da haɗa kai da ƙawayenta, ciki har da Houthi da ke Yemen da wasu ƙungiyoyin a Iraki.

Source: Getty Images
Wani jami'in Iran da ke Tehran ya ce hare-haren Amurka ne suka taimaka wajen tilasta wa ƙasarsu inganta dabarun amfani da makamai.
Iran ta yi garan bawul a harkokinta
Jerussalem Post ta wallafa cea jami'in kasar Iran ya ce yanzu sojojin Iran na iya gyarawa da inganta wuraren harba makamai cikin ƙasa da mintuna 30.
A bayanin da ya yi, ya kara da cewa a baya, irin wannan aikin na iya ɗaukar kusan sa'o'i 15 bayan harin da aka kai musu.
An bayyana cewa wannan na nuna cewa Iran na ƙoƙarin rage tasirin hare-haren da ake kai wa wuraren da take harba makamai.
Trump na so Iran ta biya diyya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai nemi Iran ta biya diyya kan mutuwar dubban sojojin Amurka da fararen hular Iran da aka kashe cikin shekarun baya.
Trump ya ce matakin na daga cikin abubuwan da ke nuna cewa tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen yaƙin da sake buɗe mashigar Hormuz na fuskantar tsaiko.
Ya kuma bayyana cewa buƙatar ta biyo bayan ikirarin masu shiga tattaunawar Iran na neman a biya su diyya kan barnar da yaƙin watanni biyar ya haddasa wa ƙasar.
Asali: Legit.ng
