"Ba Gobe ba ne"; Atiku Ya Yi Muhimmin Kira ga Matasan Najeriya

"Ba Gobe ba ne"; Atiku Ya Yi Muhimmin Kira ga Matasan Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ba matasan Najeriya shawarwar
  • Atiku ya ce matasa su yi rajista, su tsara kansu tare da shiga harkokin siyasa domin samun damar jagorantar ƙasar
  • Ya kuma ce matasa su nemi mukaman siyasa, su riƙa tambayar shugabanni abin da suke yi da amanar da aka damka a hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi muhimmin kira ga matasa.

Atiku ya bukaci matasan Najeriya su daina tsaya wa kan yin korafi game da rashin kyakkyawan shugabanci, su shirya karɓar ragamar shugabanci gabanin babban zaɓen 2027.

Atiku ya ba matasa shawara
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taron matasan ADC a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya yi wannan kira ne ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026 yayin da yake jawabi a taron koli na shugabannin matasan ADC na ƙasa da aka gudanar a Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya yi gargadi mai zafi ga INEC, Tinubu kan zaben Osun

Dan takarar shugaban kasar ya bukaci matasan Najeriya su yi rajista, su tsara kansu tare da taka rawar gani a harkokin siyasa, jaridar The Punch ta kawo labarin.

“Kada ku tsaya kawai kuna korafin mutanen da suke yanke shawara. Ku shirya kanku domin maye gurbin waɗanda suke gaza muku,” in ji Atiku.

Atiku ya ce lokacin matasa yanzu ne

Atiku ya ce shekaru da dama ana gaya wa matasan Najeriya cewa su ne shugabannin gobe, yana mai jaddada cewa an yi wa matasa alkawarin “gobe” na tsawon lokaci.

“Lokacinku ba gobe ba ne. Lokacinku yanzu ne,” in ji shi.

Ya ce manufarsa ga matasa ba wai kawai neman goyon bayansu ga burinsa na shugaban ƙasa ba ce, illa ƙarfafa musu gwiwa su mallaki makomar ƙasar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya soki yadda ake amfani da matasa wajen gangamin yaƙin neman zaɓe, amma a ware su daga yanke shawara bayan kammala zaɓe.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi? An tsage gaskiya

Ya ce matasa sun daɗe suna kasancewa masu amfani ga ’yan siyasa a lokacin yaƙin neman zaɓe, amma bayan zaɓe sai a mayar da su gefe.

A cewarsa, ana tara matasa domin cika wuraren taruka, mamaye kafafen sada zumunta da kare shugabannin siyasa, amma bayan nasara sai su gano cewa har yanzu ana yanke muhimman shawarwari a ɗakunan da ba sa cikin su.

Ya yi alkawarin ba matasa gurbi

Atiku ya yi alkawarin cewa shirin siyasarsa zai samar da gurbi na musamman ga matasa a shugabanci.

Ya ce aƙalla 30% na ’yan takarar majalisa ƙarƙashin jam’iyyar za su kasance ‘yan ƙasa da shekara 40, yayin da adadi mai yawa daga cikinsu zai kasance ‘yan ƙasa da shekara 30.

Sai dai ya bukaci matasan su shirya kansu domin ɗaukar nauyin shugabanci.

“Buɗe ƙofa kaɗai bai isa ba idan waɗanda suka shiga ba su shirya jagoranci ba. Dole ku yi nazarin yadda gwamnati ke aiki, ku fahimci harkokin kuɗaɗen gwamnati da manufofi, ku koyi yadda hukumomi ke aiki, ku fahimci al’ummomin da kuke son wakilta sannan ku shirya kanku domin wahalhalun shugabanci,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Obi, Kwankwaso sun zauna da yan takarar gwamna 25 a NDC

Atiku ya ba matasa shawara
Atiku Abubakar da sauran mutane a wurin taron matasan ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya bukaci su daina siyasar kafafen sada zumunta

Atiku ya kuma bukaci matasan su wuce matakin fafutuka a kafafen sada zumunta, su zama tsararrun masu shiga harkokin siyasa.

“Fushi ba tsari ba ne. Hashtag ba tsari ba ne. Yin korafi a kafafen sada zumunta ba tsari ba ne."

“Idan kuna son ikon siyasa, dole ku tsara kanku domin samun ikon siyasa. Ku shiga mazabun ku, ku halarci taruka, ku yi tambayoyi, ku nemi a yi wa shugabanni hisabi sannan ku shiga zaɓen waɗanda za su wakilce ku,” in ji shi.

Atiku ya gargadi INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), hukumomin tsaro da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya gargade su kan mayar da zaben gwamnan Osun tamkar aikin soja ko amfani da hukumomin gwamnati domin amfanin jam’iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng