Yadda Aka Shirya Amfani da Boko Haram, JTF domin Kifar da Gwamnatin Tinubu

Yadda Aka Shirya Amfani da Boko Haram, JTF domin Kifar da Gwamnatin Tinubu

  • Takardun bincike sun nuna masu zargin yunkurin juyin mulkin 2025 sun shirya daukar tuba-tubabben Boko Haram da mambobin CJTF domin taimaka musu.
  • Ana zargin Kanal Mohammed Ma’aji ya samu shawarar daukar CJTF da tuba-tubabben Boko Haram ne daga Manjo Jamilu Ilyasu.
  • Wadanda ake tuhuma sun kalubalanci amincewa da bayanansu a kotu, suna cewa ba da son ransu suka bayar da su ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Takardun binciken sun kara bankado wasu muhimman bayanai game da yunkurin juyin mulkin gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya.

Majiyoyi sun nuna cewa wasu manyan jami'an soja da ake zargi da shirya juyin mulki sun yi shirin daukar tuba-tubabben Boko Haram da mambobin CJTF domin taimaka wa shirin.

An so amfani da Boko Haram a yunkurin juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Rahoton Premium Times ya ce takardun sun kunshi sama da shafuka 7,400, ciki har da bayanan wadanda ake zargi, bayanan asusun banki, sakonnin sirri da bayanan tarurrukan boye.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: An gano yadda malaman addini suka karbi miliyoyi amma da wani nufi

An gano yunkurin juyin mulkin ne a watan Satumban 2025 bayan kama jami'an soja 16 masu aiki. Daga baya an kama kusan mutum 40 ciki har da fararen hula.

Da farko rundunar soji ta ce an kama jami'an ne saboda rashin da'a. Sai dai daga baya hedikwatar tsaro ta amince cewa ana zarginsu da yunkurin kifar da gwamnati.

A yanzu haka jami'an sojin da ke aiki suna fuskantar shari'a a kotun soja, yayin da fararen hula da tsoffin jami'an soja ke gaban Babbar Kotun Tarayya.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da mutane shida a watan Afrilu kan zargin hannu a shirin juyin mulkin. Daga cikinsu akwai tsoffin jami'an soja da malamai.

Rahoton ya ce Kanal Mohammed Ma’aji, wanda ake zargi da jagorantar shirin, ya samu shawarar amfani da tuba-tubabben Boko Haram da CJTF daga Manjo Jamilu Ilyasu.

Ma’aji ya ce bai san ana amfani da tuba-tubabben Boko Haram a ayyukan soja ba kafin wannan shawara. Ya kuma ce ba a kammala shirin kai su Abuja ba.

Ya bayyana cewa Manjo Ilyasu ya ce yana da mambobin CJTF da ke aiki tare da rundunar 7 Division, kuma za a iya amfani da su.

Kara karanta wannan

Tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe babban jami'in soja a Najeriya

Game da batun na'urorin fashewa, Ma’aji ya ce Ilyasu ne ya ambaci cewa akwai wasu kwararrun Boko Haram da za su iya hada IED, amma ya ce ba a bukaci hakan ba.

A nasa bangaren, Ilyasu ya tabbatar da cewa shi ne ya ba da shawarar daukar mambobin CJTF. Ya ce ya tuntubi wani dan CJTF domin samar da mutanen da za su taimaka.

Rahoton ya nuna cewa wadanda ake zargi sun dauki CJTF da tuba-tubabben Boko Haram a matsayin muhimman kadara saboda kwarewarsu da kuma makaman da suke amfani da su.

Sai dai wadanda ake tuhuma sun kalubalanci amincewa da bayanansu da bidiyoyin bincike a kotu, suna cewa ba da son ransu aka karbe su ba. Prosecution kuma ta dage cewa an bi ka'ida wajen tattara hujjojin.

Yadda aka ba malaman Musulunci miliyoyi

A wani labarin, an ji cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa malaman Musulunci sun karbi miliyoyi a yunkurin juyin mulkin da aka yi a Najeriya.

Malaman addinin Musulunci da aka ambata sun shaida wa masu bincike cewa sun yi kokarin hana shi ci gaba da aikata wannan laifi.

Daya daga cikin malaman ya ce ya karbi miliyoyin Naira domin addu'a da ayyukan alheri, yana musanta cewa ya goyi bayan yunkurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.