Sanata na Kusa da Kwankwaso Ya Fara Neman Barin NDC a Kano
- Sanata Rufai Sani Hanga ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a Kano ta Tsakiya yayin da ake rade-radin cewa yana shirin ficewa daga NDC
- Hanga ya gana da shugabannin APC da Gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin kuma ya ga Bola Tinubu
- Kungiyar Kwankwasiyya ta ce ba za ta damu ba idan Hanga ya sauya sheka, tana mai cewa an ba shi tikitin takara ba tare da hamayya ba a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya fara tuntubar manyan masu ruwa da tsaki a mazabarsa gabanin yiwuwar sauya sheka daga jam'iyyar NDC zuwa APC.
Sanata Hanga ya gana da masu tsara harkokinsa daga kananan hukumomi 15 na Kano ta Tsakiya domin tattauna batun sauya sheka.

Kara karanta wannan
Magana ta fito kan zargin Obasanjo ya yi wa Tinubu aiki, an hada Obi da Kwankwaso

Source: Facebook
The Sun ta kawo labarin cewa rahotanni sun ce ya kuma gudanar da ganawar sirri da Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Hanga ya na gana wa da manyan APC
A ruwayar Daily Post, a karshen mako kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya gabatar da shi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa.
Majiyoyi sun shaida cewa sauya shekar Hanga na gab da tabbata, sai dai ana ganin zai iya sauka daga mukaminsa na Mataimakin Mai Tsawatar da Marasa Rinji a Majalisar Dattawa, kasancewar mukamin na 'yan adawa ne.
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya, Dakta Habib Saleh Mohammed, ya ce NDC da Kwankwasiyya ba za su damu ba idan Hanga ya koma APC.
Ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya ba Hanga tikitin takarar Sanata ba tare da wata hamayya ba, amma ya yi ikirarin cewa shekaru uku da rabi da ya shafe a Majalisar Dattawa ba su nuna irin amincewar da aka yi masa ba.
Su Kwankwaso sun tuntubi Hanga
A cewarsa, Hanga na shirin sauya sheka ne saboda ya kasa samun sabunta tikitin takararsa. Ya kara da cewa jam'iyyar ta yanke shawarar tsayar da wani dan takara ne domin maslahar jam'iyya, ba don cutar da shi ba.
Mohammed ya ce an tuntubi Hanga kafin a dauki wannan mataki, kuma bai nuna adawa da shi ba a lokacin, domin ana zargin yana fatan zama mataimakin dan takarar gwamna na jam'iyyar.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da Legit, daya daga cikin masu magana da yawun Kwankwasiyya, Mansur Kusugu ya bayyana cewa bai kamata Hanga ya daga maganar sauya.
Ya ce:
"Lokacin da aka ba shi takara, ba ko sisinsa, amma yanzu idan aka ba wani ma ya samu bai kamata ya yi magana ba."
NDC ta mayar wa Hanga martani
A baya, mun wallafa cewa shugaban jam'iyyar NDC na shiyyar Arewa, Muhammad Rabi'u Bakin Zuwa, ya mayar da martani ga kalaman Sanata Rufa'i Sani Hanga wanda ya soki Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan
Sai bango ya tsage: Yadda APC ke ta yi wa Kwankwaso illa sakamakon rikicin NDC a Kano
Ya ce ba su taba gaya wa Sanata Hanga cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya aike su gidansa ba a lokacin da aka yi zancen takarar Mustapha Kwankwaso, kuma an samu goyon bayansa.
Wannan martani na zuwa ne bayan wadansu zarge-zarge da Sanata Rufa'i Hanga ya yi game da takarar gwamna da na mataimakin gwamnan Kano a NDC, inda ya ce an yi yunkurin bayar da takara da dan Kwankwaso.
Asali: Legit.ng
