Peter Obi Ya Gana da Madugun Kwankwasiyya, Kwankwaso Ya Kira Shi da Sabon Suna
- Jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta tantance Peter Obi a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben shekarar 2027
- Bayan kammala aikin tantancewar, Peter Obi, ya ziyarci tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 kuma madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna kyakkyawan zato ka sabuwar jam'iyyarsu ta NDC yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya kai ziyarar ban-girma ga Sanata Rabiu Kwankwaso.
Peter Obi ya ziyarci madugun na Kwankwasiyya ne kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a daren ranar Talata, 19 ga watan Mayun 2026.

Source: Twitter
Kwankwaso ya gana da Peter Obi
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026, Kwankwaso ya tabbatar da ganawar tasu a gidansa da ke Maitama a Abuja.

Kara karanta wannan
2027: Tsohon gwamnan Ebonyi zai jagoranci kwamitin tantance masu neman takara a NDC
Jagororin biyu na NDC sun gana ne jim kaɗan bayan da kwamitin tantancewa na jam’iyyar ya tantance Obi domin takarar zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa gabannin babban zaɓen 2027.
Hotunan ganawar sun nuna tsofaffin gwamnonin biyu zaune tare a cikin yanayi na natsuwa, suna tsaka da tattaunawa.
Kwankwaso ya kira Obi dan uwana
Kwankwaso ya bayyana Obi a matsayin “ɗan uwana” kuma ya nuna kyakkyawan zato game da makomar jam’iyyar NDC.
“A daren jiya, na karɓi ziyarar ban-girma daga ɗan uwana, Mai girma Peter Obi, jim kaɗan bayan nasarar tantance shi a matsayin mai neman takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarmu, NDC. Makomar tana da haske da kuma cike da alƙawari."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Ziyarar tana zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Obi da Kwankwaso suka shiga jam’iyyar NDC a hukumance a farkon watan Mayu, 2026, biyo bayan ficewarsu daga ADC.
Kwankwso da Obi sun hade don zaben 2027
Wannan mataki ana kallonsa a matsayin wani gagarumin sake fasalin ƙawance a siyasancin hamayya na Najeriya gabannin zaɓubbukan 2027, tare da jita-jitar cewa mutanen biyu ka iya tsayawa takara a kan tikitin haɗin gwiwa na shugaban ƙasa.

Source: Twitter
A ranar Talata, 19 ga watan Mayun 2026, kwamitin tantancewa na NDC ya tantance Obi ba tare da wani mai ƙalubalantarsa ba bayan da aka ruwaito cewa shi ne kaɗai mai neman takara da ya sayi fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Shugabannin biyu, waɗanda suka fafata a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyu daban-daban, sun kasance suna gudanar da tattaunawa kan ƙarfafa hamayya da jam’iyya mai mulki ta APC.
Kwankwaso zai samu takara a NDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan makomarsa a NDC.
Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar samun tikitin mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027.
Kwankwaso ya bayyana takarar da za a ba shi a NDC, a matsayin wacce za ta bude wa wa Kano kofar samar da shugaban kasa a nan gaba.
Asali: Legit.ng
