Kwankwaso Ya Yi Magana, Za a ba Shi Tikitin Takarar Mataimakin Shugaban Kasa a 2027
- Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi ikirarin cewa za a yi zaben da ba a taba irinsa ba a jihar Kano da Najeriya baki daya
- Kwankwaso ya ce yana da yakinin za a ba shi takarar mataimakin shugaban kasa a NDC, wanda zai bude wa Kano kofar samar da shugaban kasa
- Ana hasashen cewa Peter Obi ne zai yi takarar shugaban kasa a inuwar NDC a zaben 2027 yayin da Madugun Kwankwasiyya zai zama abokin gami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar samun tikitin mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027.
Kwankwaso ya bayyana wannan takara da za a ba shi a NDC, a matsayin wacce za ta bude kofar wa Kano kofar samar da shugaban kasa a gaba.

Kara karanta wannan
"Shirun da muka yi ba tsoro ba ne," Gwamna Abba ya tura zazzafan sako ga Kwankwaso

Source: Facebook
Takarar da Rabiu Kwankwaso zai samu a NDC
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Premier Radio a karshen makon da ya gabata.
“Idan Allah ya yarda, za a yi zaben da ba a taba irirnsa ba a jiharmu da ma kasa baki daya, musamman idan Allah ya sa na samu wannan tikitin takara kuma sunana ya shiga takardar zabe.
“Tun da aka soma dimukuradiyyar nan, tun jamhuriya ta farko, duk yawan nan namu da wahalar da muka yi da hikimar siyasa da muke da ita, Kano ba ta taba samar da mataimakin shugaban kasa ba.
"Wannan abin takaici ne kuma abin bakin ciki, amma da yardar Allah za a gyara shi, jihar Kano za ta samu wannan mukami, kuma hakan zai bude kofar da jiharmu za ta samar da shugaban kasar nan a gaba.”
- Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya ja hankalin 'yan Arewa
Ya kuma ce mutane daga kudancin Najeriya da suka fahimci abin da ke faruwa suna ci gaba da shiga jam’iyyar tasu, yana mai kira ga Arewa, musamman Arewa maso Yamma, da su farka daga barci.
“Mutanen Kudu da suka fahimci abin da ke faruwa suna shiga jam’iyyarmu. Arewa musamman Arewa maso Yamma dole ta kula sosai domin kada ta dauki matakin da daga baya za ta yi nadama,” in ji shi.
Kwankwaso da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, sun koma jam’iyyar NDC a farkon watan nan.
NDC za ta ba Obi/Kwankwaso takara
Rahotanni sun nuna cewa Obi da Kwankwaso sun shiga jam’iyyar NDC ne bisa yarjejeniyar tsayawa takarar shugaban kasa tare
Ana sa ran Obi zai tsaya takarar shugaban kasa yayin da Kwankwaso zai zama mataimakinsa a zaben 2027, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Source: Facebook
A Najeriya dai an dade ana bin tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu wajen shugabancin kasa, inda mutane da dama ke ganin cewa ya kamata wani dan Kudu ya kammala wa’adin shekaru takwas kafin mulki ya koma Arewa a 2031.

Kara karanta wannan
Magana ta fito, an ji abin da Tinubu ya shirya yi a shekaru 2 na farko bayan ya ci zaben 2027
Kwankwaso ya nuna cewa idan aka zabi Obi a matsayin shugaban kasa a 2027 kuma shi ya zama mataimakinsa, hakan zai ba shi damar neman shugabancin kasa a shekarar 2031.
Dalilin hadewar Kwankwaso da Obi
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce haɗakarsa da Peter Obi ba ta da alaƙa da addini ko yanki, illa ceto Najeriya.
Ya ce bangarorin biyu sun fahimci cewa suna da manufofi iri ɗaya wajen samar da ingantaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya, musamman matasa.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa jam’iyyarsu ta NDC tana ƙoƙarin zama wata sabuwar mafita ga ‘yan Najeriya kafin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
